Gobara Ta Tashi a Gidan Shehu Shagari Tsohon Shugaban Kasar Najeriya

Gobara Ta Tashi a Gidan Shehu Shagari Tsohon Shugaban Kasar Najeriya

  • Gobara ta tashi a wani daga cikin gidajen marigayi Alhaji Shehu Shagari, tsohon shugaban kasar Najeriya
  • Lamarin ya faru ne misalin karfe 11 na safiyar ranar Lahadi 19 ga watan Nuwamba a unguwar Gobirawa da ke Sokoto
  • Rahotanni sun nuna cewa an yi asarar dukiya da kadarori masu daraja a gidan da akalla yan uwan marigayin kimanin su 20 ke zaune

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Sokoto - Kadarori da abubuwa masu amfani sun kone a wani sashin gida mallakar marigayi Alhaji Shehu Shagari, tsohon shugaban kasar Najeriya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa gobarar ta tashi ne misalin karfe 11 na safiyar ranar Lahadi 19 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Gobirawa a Sokoto.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Manjo Janar Chris Alli rasuwa

Gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Shehu Shagari.
Gobara ta lalata kadarori da dukiya a gidan Alhaji Shehu Shagari da ke Sokoto. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa akwai akalla mutane 20 yan uwan marigayin tsohon shugaban kasan a cikin gidan.

A cewar wadanda abin ya faru a kan idonsu, kadarori da dama mallakar iyalan maraigayi shugaban kasar sun kone a gobarar, amma ba a rasa rayuka ba.

Jikan Shagari ya tabbatar da afkuwar lamarin

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, Attahiru Shehu, jikan Shagari, ya ce yana gida a lokacin da abin ya faru. Attahiru ya ce ya ji mutane suna neman dauki domin a taya su kashe wutan.

Shagari ne mutum na farko da aka fara zaba a matsayin shugaban kasa karkashin dimokradiyya. Ya rike mukamin daga 1979 zuwa 1983 lokacin da aka mas juyin mulki.

Ya rasu yana da shekaru 92 a ranar 28 ga watan Disamban 2018.

Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan gobarar da gidansa ya yi, hotuna sun bayyana

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

A wani rahoton daban shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya siffanta gobarar da ya tashi a wani sashin gidansa a matsayin ikon Allah.

Shaihin malamin ya kara da cewa kawo yanzu ba a gano abin da ya yi sanadin gobarar ba, don lokacin da abin ya faru babu wutar lantarki, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Tunda farko, wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce gobarar ta fara ci ne a sashin makarantar Islamiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel