Wata Mata Ta Yi Yaji Bayan Sun Samu Sabani da Mijinta, Ya Je Biko da Tsinken Tsire 2

Wata Mata Ta Yi Yaji Bayan Sun Samu Sabani da Mijinta, Ya Je Biko da Tsinken Tsire 2

  • Wata mata ta yi yaji daga gidan mijinta bayan sun samu sabani sannan shi kuma ya bi ta dauke da gasasshen nama don yin biko
  • Wannan bidiyo mai ban mamaki ya nuna yadda wani mutum ya yi kokarin dawo da soyayyarsa a wajen batarsa da tsinken tsire guda biyu
  • Matar ta koma gidan diyarta ne bayan ta tattara kayanta sannan ta yi yaji daga gidansu

Wani bidiyo mai ban dariya na sabanin ma'aurata da sulhunsu ya yadu a dandalin soshiyal midiya.

Ya nuna yadda miji ya yi baikon matarsa wacce ta yi yaji bayan sun samu zazzafan sabani a tsakaninsu da tsire.

Miji ya yi bikon mata da tsiken tsire
Wata Mata Ta Yi Yaji Bayan Sun Samu Sabani da Mijinta, Ya Je Biko da Tsinken Tsire 2 Hoto: TikTok/@mila_mcjohn0
Asali: TikTok

Matar ta tattara kayanta sannan ta fice daga gidansu, inda ta nemi mafaka a gidan diyarta.

Mijin, wanda ya yi nadama sannan ya so ganin abubuwa sun daidaita tsakaninsa da matarsa, ya bi ta can gidan da tsinken tsire biyu a hannunsa.

Kara karanta wannan

“Kasuwa ta yi kyau”: Mabaraciya ta siya soyayyar kaza, ta darje ta zabi wanda take so

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mijin ya bai wa matar tasa hakuri domin ta yafe masa sannan ta koma dakinta, yayin da ya fito da tsinken tsiren don gabatar mata da su a matsayin tukwicin sulhu.

Matar, wacce alamu suka nuna tayi mamaki da jin dadin wannan karamci nasa, ta yarda da hakurin da ya bata da kuma tsiren. Bidiyon ya tsuma zukatan masu kallo da dama wanda abun ya basu dariya da kuma sha'awa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon

Stephanie ta yi martani:

"Ina ma ace haka na girma da ganin irin wannan soyayyar."

Bae-kae:

"Toh Tsire ya zama furan yan Najeriya? Ina son shi."

Somto ta ce:

"Ganin cewa da gaske ya siya mata tsire."

Fhayfhay:

"Jan hajin Mumi kamar hakan ba dadi ya yi mata ba."

Gloria Jonathan:

Kara karanta wannan

“Na sha kuka”: Yar Najeriya ta yada hirar da ta gani a wayar mijinta

"Allah yasa mazajenmu su so mu haka, Amin."

MhizPraiz:

"Iyayena sun samu sbaani sannan mahaifiyata ta bar gidan, kannena maza sun bi mahaifiyarmu amma ni na tsaya da mahaifina, amma mutumin nan sai ya yi ta zuwa sabon gidanta yana cin abinci."

Anyi likin fitar hankali a wani taro

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyon TikTok ya ja hankalin dubban masu kallo, yayin da ya nuno mutane suna kwashewa da tattara kudade masu yawan gaske daga kasa bayan kammala wani babban taro.

Alamu sun nuna taron wani kasaitaccen biki ne aka yi wanda ya samu halartan manyan masu fada aji da masu hannu da shuni da suka bude bakin aljihu suka zazzagawa ma'auratan don taya su murna da san barka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel