“Ruwan Zuma”: Ma’aurata Yan Unguwar Mallam Shehu Sun Baje Kolin Soyayya a Gaban Gidansu, Bidiyon Ya Yadu

“Ruwan Zuma”: Ma’aurata Yan Unguwar Mallam Shehu Sun Baje Kolin Soyayya a Gaban Gidansu, Bidiyon Ya Yadu

  • Jama'a sun yi cece-kuce bayan bayyanar bidiyon wasu ma'aurata da ke rayuwar jin dadi a tsakaninsu
  • Ba tare da duba yanayin unguwar da suke ba, ma'auratan cikin shigarsu ta daidai ruwa daidai tsaki sun yi sharholiyarsu a gaban wani gidan jan laka
  • Mutane da dama sun nuna sha'awarsu ga soyayyar da ma'auratan ke yi wa junansu, inda suka bayyana shi a matsayin soyayya ta gaskiya

Wani bidiyo na wasu ma'aurata da ke sharholiya da jin dadin kasancewarsu tare a gaban wani gidan jan laka ya yadu a TikTok.

Dauke da murmushi kan fuskokinsu, ,masoyan sun taka rawa tare da runguma da kuma sumbatar junansu yayin da suke sanye da tufafinsu na yau da kullun.

Ma'aurata suna shan soyayya
“Ruwan Zuma”: Ma’aurata Yan Unguwar Mallam Shehu Sun Baje Kolin Soyayya a Gaban Gidansu, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @earthquakekisaka1
Asali: TikTok

Bidiyon ma’auratan ya ja hankalin mutane miliyan daya da suka kalle shi, inda da dama suka nuna sha’awarsu kan soyayya ta gaskiya da suke nunawa junansu.

Kara karanta wannan

“Soyayya Bata Tsufa”: Tsohuwa Mai Dogara Sanda Ta Amarce Da Sahibinta, Bidiyon Ya Yadu

Shafin ma’auratan ya nuna yadda suke daura bidiyoyinsu a wurare don nishadantar da mabiyansu,. Shafinsu na TikTok, @earthquakekisaka1, yana da mabiya fiye da 157k.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Perrie ta ce:

"Sun matsa daga jajin yanzu kusa da gado muna gab da isa wajen."

Steve Benz007 ta ce:

"Idan kana son sanin yadda kakanninka suke soyayya, haka yake."

Queenie ta ce:

"Ina bukatar irin wannan soyayyar."

mavisyevu45 ta ce:

"Na tsaya a inda yake shirin sumbatarta don karanta martanin jama'a."

_iamchaeofficial01 ya ce:

"Malamai ga soyayya ta gaskiya a nan wajen."

lizug45 ta ce:

"Shin kun lura cewa a koda yaushe mutumin nan da wannan kayan yake sanye."

user1988912842365 ya ce:

"Matsin lambar na yawa a garemu mu da bamu da aure har yanzu."

Kara karanta wannan

“Ta Gaji Da Auren Tun Ba a Kai Koina ba” Bidiyon Amarya Tana Kicin-Kicin Da Rai Yayin da Take Jerawa Da Angonta Ya Yadu

Ba zan so saurayi ba sai yana da N2m a asusun banki, matashiya

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta gindaya sharadin da sai saurayi ya cike kafin ta yarda ta yi soyayya da shi.

Budurwar wacce ta ce N3k ne kacal a asusun bankinta ta ce sai saurayi ya mallaki akalla miliyan N2 a asusun bankinsa kafin ma ta yarda su yi soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel