Bidiyon Wasu Ma’aurata da Suka Shafe Shekaru 45 da Aure Ya Dauka Hankali, Mijin Bature Ne

Bidiyon Wasu Ma’aurata da Suka Shafe Shekaru 45 da Aure Ya Dauka Hankali, Mijin Bature Ne

  • Bidiyon wasu ma'aurata bature da bakar fata ya matukar burge masu amfani da soshiyal midiya inda suka roki Allah ya basu irin nasu
  • Ma'auratan sun ba da labarin soyayyarsu wacce ta fara tun shekaru 45 da suka shige lokacin da suka yi aure
  • Hadadden bidiyon ya samu mutum fiye da miliyan 6 da suka kalla a TikTok cikin mako daya da wallafa shi a shafinsu

Wasu ma'aurata wadanda suka kasance tare da juna duk rintsi duk wuya sun yi murnar cika shekaru 45 da aure.

Sun wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda suka yi rayuwa tare tsawon shekaru a shafinsu na TikTok mai suna @jeriandmike.

Ma'aurata
Bidiyon Wasu Ma’aurata da Suka Shafe Shekaru 45 da Aure Ya Dauka Hankali, Mijin Bature Ne Hoto: @jeriandmike
Asali: UGC

Bidiyon mai ratsa zuciya ya yadu a soshiyal midiya kuma soyayyarsu ta burge jama'a daga fadin duniya.

A bidiyon, an gano Jeri da Mike cikin farin ciki yayin da suke tsufa tare bi da bi shekaru bayan shekaru.

Kara karanta wannan

Doguwar Mace Alkyabbar Mata: Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Mai Tsawon Inci 6.5 Ya Yadu a TikTok

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane sun yi martani cewa ma'auratan sun karfafa masu gwiwar cewa har yanzu akwai soyayya ta gaskiya kuma sun yi ma ma'auratan fatan alkhairi.

Jeri da Mike na da mabiya fiye da 130k a TikTok wadanda suke jin dadin yadda suka karkata wajen nishadantar da mutane da soyayya da zamantakewarsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@cebastianos ta wallafa:

"Wannan irin kyawawan ma'aurata. Lallai kyawu mara gushewa."

@offended24.7 ya ce:

"Wannan ya sa zuciyata murmushi, ina yi maku fatan wasu shekaru 100 tare."

@harryprice201 ya ce:

"Wannan irin labarin soyayya mai kyau."

@dalibramorris ta ce:

"Na yi matukar farin ciki cewa kun ci nasara."

Uban amarya ya gwangwaje mijin diyarsa da dalleliyar mota

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani matashin ango ya hadu da karamci irin na surukin kirki inda ya yi masa wani gagarumin kyauta domin nuna godiya a kan auren diyarsa da ya yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wani Mai Sahgo da Mahaukaciya ya ba jama'a Mamaki, SUn Dinga Hira kamar Tsofaffin Masoya

Uban amaryar wanda ya kasance attajirin dan kasuwa kuma mai taimakon al'umma a kasar Zambiya, ya baiwa surukin nasa kyautar dalleliyar mota kirar Land Rover a wajen shugalin bikinsu.

Mutane da dama da suka yaba da wannan karamci na uban amaryar sun shawarci angon da ya rike ta hannu bibbiyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel