Gungun Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Zauren Majalisar Tarayya, Sun Nemi a Tsige Minista 1 Rak

Gungun Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Zauren Majalisar Tarayya, Sun Nemi a Tsige Minista 1 Rak

  • Wasu ƴan gwagwarmaya sun mamaye majalisar dokokin tarayya suna neman a tsige ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle
  • Masu zanga-zangar sun buƙaci shugaban majalisar dattawa ya takura wa shugaban ƙasa ya sauke Matawalle daga muƙaminsa
  • A cewarsu, suna zargin tsohon gwamnan yana da alaƙa da ƴan bindiga da suka addabi mutane

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Daruruwan masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya sun fita tattaki da zanga-zangar lumana zuwa majalisar tarayya da ke Abuja ranar Laraba.

Masu zanga-zangar sun nemi a gaggauta tsige ƙaramin ministan tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Masu Zanga-Zanga a Abuja Sun Nemi a Tsige Ministan Tsaro Bello Matawalle Hoto: Bello Matawalle
Asali: Facebook

Masu zanga-zangar a harabar zauren majalisar sun riƙa rera waƙoƙin haɗin kai kana suka ɗaga tutoci masu rubutu daban-daban kamar, "A kori Bello Matawalle yanzu."

Kara karanta wannan

FUGUS: Ɗalibai mata na jami'ar arewa da aka ceto daga hannun ƴan bindiga sun samu tallafi mai tsoka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka sun ɗaga allon da ke ɗauke da rubutun, "Kuɗin tsaron mu ba su da tsaro." da sauran makamantansu, kamar yadda Vanguard ta ruqaito.

Daga cikin sauran abubuwan da suka nuna damuwa, masu zanga-zangar karkashin kungiyar Civil Society Advocacy Groups for Accountability and Probity sun zargi Matawalle da, "ɗasawa da ƴan bindiga."

Sun aike da sako ga Akpabio

Jagoran tawagar masu zanga-zangar, Danesi Momoh, ya yi jawabi ga ƴan jarida a gaban majalisar, inda ya tura sako ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Ya yi kira ga shugaban majalisar dattawa ya matsa wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, lamba domin ya sauke Matawalle daga muƙaminsa.

A kalamansa ya ce:

"Tsarin tsaro da ɗora jagora mara inganci na ɗaya daga cikin kuskuren wannan gwamnatin, amma za a iya gyara kuskuren idan majalisar dattawa ta ɗaga murya ta hanyar da ta dace."

Kara karanta wannan

"Ina da bidiyo" Sanata ta tona asirin gwamnan arewa, ta faɗi yadda ya yi yunƙurin kashe ta

"Muna kira ga Majalisar Dattawa ta tashi tsaye ta tabbatar da an tsige shi cikin gaggawa domin dawo da fatan ƴan Najeriya na samun shugabanci na gari."

Da yake martani kan zanga-zangar, Darakta a Majalisar ta kasa, Salihu Abdullahi, wanda ya karbi takardar koken a madadin Akpabio, ya nuna jin daɗin yadda aka yi zanga-zangar cikin lumana.

Ya kuma yai musu alkawarin cewa zai miƙa dukkan koken da suka gabatar da waɗan da ya dace.

Bam.ya tashi a Yobe

A wani rahoton kuma Akalla mutanen kauye 20 ne suka rasa rayuwarsu yayin da wani babur ya tashi da bam din da kungiyar Boko Haram ta dasa a jihar Yobe.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun dawo daga makokin matasa 17 da aka kashe a yankin ƙaramar hukumar Gaidam ranar Litinin, lokacin da Bam ɗin ya tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262