Rundunar ’Yan Sanda: Abin Da Ya Sa Jami’anmu Suka Watsawa Gwamna Ruwan Zafi da Barkonon Tsohuwa

Rundunar ’Yan Sanda: Abin Da Ya Sa Jami’anmu Suka Watsawa Gwamna Ruwan Zafi da Barkonon Tsohuwa

  • Rundunar 'yan sanda ta watsa wa gwamnan jihar Ribas da tawagarsa ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye
  • Gwamnan jihar Ribas, ya ce wannan 'harin' da rundunar 'yan sanda ta kai masa alama ce ta samun bara-gurbi a hukumar tsaron jihar
  • Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta ce watsa wa gwamnan ruwan zafi da borkokon tsohuwa ba da gan-gan bane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ribas - Rundunar 'yan sandan jihar Ribas, shiyyar Kudu maso Kudu, ta bayyana dalilin da ya sa jami'anta, a ranar Litinin, suka harba borkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi ga gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a garin Fatakwal yayin wata tarzoma da ta barke biyo bayan wani yunkuri na tsige gwamnan da aka yi.

Kara karanta wannan

"Ba matsala ne ba idan an samu rashin jituwa tsakanin ɗa da mahaifi", Gwamna Fubara

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara
Rundunar 'yan sanda sun bayyana dalilin watsa wa Gwamnan Ribas borkonon tsohuwa Hoto: Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda jami'an rundunar 'yan sandan suka watsa borkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi kai tsaye ga Mr Fubara, wanda ke karkashin rakiyar wasu jami'an tsaro da matasa.

A lokacin da lamarin ya faru, gwamnan tare da tawagar magoya bayansa na tafiya ne kan titi da nufin zuwa ginin majalisar dokokin jihar, inda wani bangare na ginin ya lalace sakamakon fashewar wani abu a ranar da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Gwamna Fubara ya ce game da wannan harbi

Sakamon watsa masa borkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi, Mr Fubara, ya ce an samu bara-gurbi a cikin jami'an tsaron jihar.

Suna harba hayaki mai sanya hawaye da ruwan zafi kai tsaye gare ni. Amma wannan ba wani abu bane, dole ne sai mutum ya mutu komai daren dadewa.

Tuni dai rundunar 'yan sanda ke samun matsin lamba kan ta fito ta yi bayanin dalilin kai wa gwamnan wannan hari.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP za su gana da Ministan Tinubu kan muhimmin batu 1, bayanai sun fito

Dalilin 'Yan Sanda na watsawa Gwamna Fubara ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta ce Gwamna Fubara na tsakiyar wasu 'fusatattun' mutane da ke tunkarar ginin majalisar jihar Ribas, cewar Leadership.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ce ta sanya wa sanarwar hannu a madadin kwamishinan rundunar na jihar, Polucarp Emeka

Rundunar ta kuma ce ta yi amfani da borkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi ne domin tarwatsa zanga zangar da fusatattun mutanen ke yi, da ke neman wuce gona da iri.

A cewar sanarwar:

Ganin gwamna a cikin wadannan fusatattun matasa ya bamu mamaki matuka, kasantuwar babu wani sako da rundunar 'yan sandan ta samu na cewar gwamnan zai ziyarci wajen.
Sanar da rundunar 'yan sandan zuwan nasa shi ne tsarin da ake bi, domin bashi kariya, la'akari da halin tashin tashinar da ake ciki a lokacin. Amma ba mu samu wata masaniya akan zuwan nasa ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta shiga tsakani a rigimar Gwamna Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas

Gwamnonin PDP Sun Sa Labule da Ministan Bola Tinubu, Bayanai Sun Fito

Tawagar gwamnonin jam'iyyar PDP karkashin ƙungiyasu na gana wa yanzu haka da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a ofishinsa da ke Abuja.

Gwamnonin sun sa labule da Wike ne karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed (Ƙauran Bauchi).

Asali: Legit.ng

Online view pixel