Bam Ya Tashi da Masu Zuwa Jana'iza, Mutane Sama da 20 Sun Mutu a Jihar Yobe

Bam Ya Tashi da Masu Zuwa Jana'iza, Mutane Sama da 20 Sun Mutu a Jihar Yobe

  • Ana zargin mayaƙan Boko Haram sun dasa wa masu zuwa jana'iza bam a jihar Yobe kuma aƙalla mutane 20 suka mutu nan take
  • Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun dawo daga makokin matasa 17 da aka kashe a yankin ƙaramar hukumar Gaidam ranar Litinin
  • Wani mazaunin yankin ya ce tun da daddare suka fara jana'izar mamatan kuma za a ƙarisa da safiyar ranar Laraba

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Akalla mutanen kauye 20 ne suka rasa rayuwarsu yayin da wani babur ya tashi da bam din da kungiyar ta'addanci watau Boko Haram ta dasa a jihar Yobe.

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, abun fashewar ya tashi da mutanen ne ranar Talata da misalin ƙarfe 6:30 na yammaci.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 12 a jihar Zamfara

Bam ya tashi da jama'a a jihar Yobe.
Yanzu-Yanzu: Bam Ya Tashi da Masu Zuwa Jana'iza, Mutane Sama da 20 Sun Mutu a Jihar Arewa Hoto: Leadership
Asali: UGC

Wannan lamari ya faru ne a ƙauyen Goni Mittiri da ke yankin garin Gumsa a ƙaramar hukumar Gaidam, jihar Yobe a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa masu zaman makoki a kauyen mai tazarar kilomita 20 daga garin Gaidam, sun tafi jana’izar mutane 17 da harin Boko Haram ya rutsa da su lokacin da lamarin ya faru.

Rahoto ya nuna a hanyar dawowwa daga wurin jana'izar mutanen da Boko Haram ta kashe ne Bam ɗin ya tashi da su, ya kashe aƙalla mutum 20.

A cewar ganau, ƴan ta'addan sun dasa Bam ɗin a kan hanyar da mutane ke bi suna wucewa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rayukan da aka rasa a tashin bam ɗin

Wani mazaunin garin da lamarin ya faru ya bayyana cewa:

"Mun ƙirga gawarwakin mutane 20 nan take a wurin da lamarin ya faru, zamu yi wa mutane 11 daga ciki jana'iza da daren nan (ranar Talata)."

Kara karanta wannan

Rayukan mutum 3 sun salwanta a wani kazamin hatsarin mota a jihar Legas

"Sauran kuma sai Allah ya kaimu gobe Laraba da misalin ƙarfe 9:00 na safiya zamu musu jana'iza."
"A halin yanzu wasu ma'aurata mata da miji suna kwance a Asibiti ana musu maganin raunukan da suka ji a tashin bam ɗin."

Zulum ya hango matsala

A wani rahoton na daban Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ce matuƙar ba a magance Boko Haram da ISWAP ba, zasu iya shafe taswirar Najeriya.

Gwamnan ya ce ƙungiyoyin ƴan ta'addan ka iya amfani da sansanonin ƴan gudun hijira a matsayin wurin ɗaukar mayaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel