Nyesom Wike Ya Farfado da Doka, Marasa Biyan Haraji Za Su Tafi Kurkuku a Abuja

Nyesom Wike Ya Farfado da Doka, Marasa Biyan Haraji Za Su Tafi Kurkuku a Abuja

  • Ezenwo Nyesom Wike ya na so a tabbatar da dokar biyan haraji ta na aiki a birnin Abuja domin asamu kudin shiga masu yawa
  • Ministan ya fitar da sanarwa cewa ma’aikatu da hukumomin banki da bankuna su rika tambayar takardar shaiar TCC ta biyan haraji
  • Duk wani wanda aka samu ya saba doka, Wike ya yi na’am da hukunta shi, hakan zai iya zama cin tarar kudi ko zaman gidan yari

Abuja - Ministan birnin tarayya watau Abuja, Ezenwo Nyesom Wike zai sake shigowa labarai kwanaki bayan an fara kiran a tsige shi.

Wannan karo, Daily Trust ta ce Barista Ezenwo Nyesom Wike ya nemi a dabbaka tsarin karbar haraji kamar yadda ya zo dokar Abuja.

Sabon Ministan ya dauki mataki ne saboda a samu kudin shiga domin yin ayyuka.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Nyesom Wike
Ministan birnin Abuja Hoto: Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Nyesom Wike zai tara kudi a Abuja

Kwanakin baya aka ji gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Bola Tinubu, ta ba FCTA damar fita daga cikin asusun TSA na bai-daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanadiyyar umarnin da ministan ya bada, duk wata ma’aikata, cibiya ko hukumar gwamnati ko banki za su dage wajen tattaro haraji.

Abuja: Dokokin haraji za su yi aiki

Umarnin ya zaburar da duka ma’aikatu da kuma bankunan kasuwa su dage musamman wajen tabbatar da sashe na 85 na dokar PITA.

Business Day ta ce umarnin ministan zai tabbatar da aikin sashe na 31 na dokar harajin birnin tarayya wanda aka fito da ita a shekarar 2015.

Dokokin sun bukaci hukuma ko banki ya nemi ganin takardar shaidar biyan haraji na TCC kafin a iya yin wani ciniki a fadin birnin na Abuja.

Kara karanta wannan

Wike: Tashin Hankali Yayin da Tsohon Kakakin APC Ya Bukaci Tinubu Da Ya Kama Sheikh Gumi

Ina hukuncin kin biyan haraji a Abuja?

Hukuncin wanda aka samu ya sabawa wannan doka ya fara ne daga tarar N100, 000.

Baya ga biyan tara, idan har laifin ya yi yawa, kotu za ta iya yankewa mutum daurin shekaru uku a gidan gyaran hali idan har ya saba doka.

Wani babban jami’in da ke kula da tsare-tsaren tattali da samun haraji, Chinedum Elechi ya shaidawa ‘yan jarida wannan a ranar Litinin.

Ana kukan tsadar rayuwa a yau

Mafi yawan al'ummar Najeriya su na faman kokawa a game da 'dan karen tsadar rayuwa kamar yadda aka samu labari a wani rahoto dazu.

Cire tallafin da aka yi ya jawo farashin man fetur ya karu da kusan N500 sannan kudin gas da ake saye domin yin girki ya tashi a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel