Tinubu Ya Tsame Babban Birnin Tarayya Daga Asusun Ajiya Na Bai-Daya

Tinubu Ya Tsame Babban Birnin Tarayya Daga Asusun Ajiya Na Bai-Daya

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tabbatar da cewar Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsame babban birnin tarayya daga asusun baitul mali na bai-daya (TSA)
  • Wike ya bayyana a taron manema labarai cewa wannan zai ba babban birnin tarayya damar amfani da kudaden shigarta don bunkasa babban birnin tarayyar kasar
  • Ministan ya yi Karin haske cewa shugaban kasar ya amince da kafa hukumar kula da ma’aikatan birnin tarayya don ci gaban ma’aikata

FCT, Abuja - Rahotanni sun kawo cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsame babban birnin tarayya daga asusun ajiyar kudi na bai daya (TSA) a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.

Tinubu ya zare FCT daga asusun ajiya na bai-daya
Tinubu Ya Tsame Babban Birnin Tarayya Daga Asusun Ajiya Na Bai-Daya Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Dalilin da yasa Tinubu ya tsame babban birnin tarayya daga asusun TSA, Wike ya magantu

Wannan mataki da shugaban kasar ya dauka ya kasance don ba gwamnatin FCTA da Nyesom Wike ke jagoranta damar amfani da kudaden shiga na yankin don bunkasa babban birnin tarayyar kasar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Jerin Sunayen Mutane 14 Da Tinubu Ya Bai Wa Sabbin Mukamai

Tinubu ya kafa sabuwar hukuma a babban birnin tarayya

Wike wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma'a a Abuja, ya kuma bayyana cewa Shugaban kasa Tinubu ya amince da kafa hukumar kula da ma’aikata ta babban birnin tarayya Abuja, domin ba da damar ci gaban aikin ma’aikata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kallon matakin a matsayin kara wa tsohon gwamnan jihar Ribas, Wike, wanda Tinubu ya nada a matsayin ministan Abuja a watan Janairu, karfi.

Da wannan mataki na cire FCTA daga asusun TSA, Tinubu na kara ba Wike damar jan ragamar kudaden yankin.

Da alama hakan zai bai wa Wike damar kara habaka ci gaban babban birnin kasar, Abuja, rahoton BusinessDay.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci hana ’yan bola jari shiga yankin Mabushi da Katampe

Kara karanta wannan

Bidiyon Ministan Abuja Wike Yana Girkawa Saraki Abinci Ya Girgiza Inatanet

A wani labarin, ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci jami’an tsaro da su hana masu baban bola da makanikai shiga yankin Mabushi da Katampe na birnin Abuja.

Wike ya bayyana haka ne a yau Talata 10 ga watan Oktoba inda ya ce mutane na amfani da wadannan wuraren don aikata laifuka, The Nation ta tattaro.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bola jari da makanikai da kafintoci na daga cikin wadanda ke kawo matsala a yankin na Mabushi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel