'Yan Ta’adda Sun Kai Farmaki Kan Ayarin Motocin Gwamnan Kogi, Ya Sha Dakyar

'Yan Ta’adda Sun Kai Farmaki Kan Ayarin Motocin Gwamnan Kogi, Ya Sha Dakyar

  • Yanzu muke samun labarin yadda wasu 'yan ta'adda suka kai farmaki kan ayarin motocin gwamnan Kogi
  • Gwamna Yahaya Bello ya sha dakyar, ya zuwa yanzu ba a bayyana asarar da aka yi a harin da aka kai masa ba
  • Ba wannan ne karon farko da ake kai hari kan dan siyasa ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa a baya

Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi a ranar Lahadi ta ce jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kisa da aka yiwa gwamnan jihar Yahaya Bello, The Nation ta ruwaito.

A cewar gwamnatin, an farmaki gwamnan ne a jiharsa da ke da tazarar kilomita kadan da babban birnin tarayya Abuja, a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki daga birnin Lokoja.

Sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar a Abuja, ya ce an kai harin ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Abin Da Cire Takunkumin CBN Yake Nufi Ga Manoma Da Abinci, Masani

An farmaki Yahaya Bello
An farmaki gwamnan jihar Kogi | Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Bayanai daga gidan gwamnati

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Maharan da ke sanye da kakin soji sun tare ayarin motocin Gwamnan, inda suka yi ta harbe-harbe kan motarsa da sauran motocin da ke cikin ayarin.
"Sai da jami’an tsaro da ke tare da gwamnan sun yi kokari ainun cikin gaggawa wajen dakile mugun nufin na sojojin da ba a san ko su waye ba.
"An kai farmakin ne har sau uku a wurare mabambanta, na karshe a kusa da Kwali da ke babban birnin tarayya da misalin karfe 4:20 na yamma."

Akwai hannun masu son kawo tsaiko a zabe

Fonwo ya kuma bayyana cewa, da gani wadannan hare-hare an jima ana tsara su, kuma jami'an tsaron da ke jihar da ma kasa baki daya sun fara daukar mataki da kuma yin bincike a kai, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Ministan Abuja Ya Sake Dauko Gingimemen Aiki, Da Yiwuwar Ya Kwace Wasu Gidaje a FCT

Ya kuma bayyana zargin cewa, harin ba zai rasa nasaba da wasu da ke son kawo tsaiko a zaben 11 ga watan Nuwamba da ke tafe a jihar ba.

An farmaki dan takarar gwamna

A bangare guda, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Murtala Yakubu-Ajaka, dan takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da Ajaka da wasu jiga-jigan SDP ke dawowa daga taron masu ruwa da tsaki a yankin Ogori Magongo.

Rahoton The Cable ya tattaro cewa ‘yan bindigan sun yi artabu da jami’an tsaro a wata musayar wuta kafin daga bisani su bar motocinsu guda biyu su gudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel