Albanin Kuri: Halin Da Iyalansa Ke Ciki Bayan Kashe Malamin A Gombe

Albanin Kuri: Halin Da Iyalansa Ke Ciki Bayan Kashe Malamin A Gombe

  • Wasu barayi sun yi ajalin wani malami, Ibrahim H Musa da aka fi sani da Albanin Kuri a gidansa da ke bayan garin Gombe
  • Malamin ya rasa ransa ne a daren ranar Talata bayan da barayin suka yi ajalinsa ta hanyar caka masa wuka a kirji
  • Legit.ng Hausa ta tattauna da iyalansa don sanin halin da suke ciki a yanzu da irin gudumawar da su ka samu

Jihar Gombe - Tun bayan kashe mashahurin malami a jihar Gombe, Sheikh Ibrahim Musa da aka fi sani da Albanin Kuri a gidansa, jami'an tsaro sun bazama neman wadanda ake zargi.

Malamin ya rasu ne a daren ranar Talata 8 ga watan Agusta bayan an dauke shi zuwa asibitin kwararru kafin daga bisani aka mika su zuwa asibitin koyarwa na Tarayya inda marigayin ya ce ga garinku.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci, Matarsa Da Yara 2, Ciki Harda Jaririn Kwana Daya

Yadda 'yan ta'adda suka kashe Ibrahim Musa da aka fi sani da Albanin Kuri
Marigayi Albanin Kuri Kenan Da Barayi Suka Kashe A Gombe. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Meye iyalan malamin ke cewa?

Legit.ng Hausa ta tattauna da yayan marigayin mai suna Dahiru Halliru kan halin da suke ciki bayan rasuwar malam.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dahiru ya ce tabbas sun samu gudumawa marar iyaka daga kungiyar Izala don a kullum cikin ba su taimako su ke.

Sai dai ya koka kan yadda daga bangaren gwamnati babu wata tawaga daga Gwamna ko kuma 'yan majalisar yankin da suka zo musu ta'aziya.

Ya ce:

"Kungiya Alhamdulillah ta yi taimako sosai don ko shekaran jiya ma ta taimaka da abinci da sauransu kuma har yanzu su na kokari.
"A gefen gwamnati kam musamman na jiha babu wani abu da za mu ce ta yi na taimakon iyalan wannan bawan Allah.
"A bangaren 'yan sanda kuma ya ce suna ba su hakuri da cewa ana kan bincike sai a hankali za a yi nasara.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: An Fadawa Tinubu Abu Daya Tak Da Zai Yi Don Shawo Kan Matsalar Tsaro A Jihar Arewa, Ta Nemi Bukata

Ya kara da cewa:

"Eh 'yan sanda suna tuntubanmu tare da ba mu hakuri cewa ana kan bincike sai a hankali, jami'an tsaro da yawa sun zo gidan ta'aziya daga fadin kasar."

Tun farko daya daga cikin matan marigayin, Fatima Muhammad Umar ta ce duk da malam ya ce ya yafe wa wadanda suka yi ajalinsa, amma su kam jinin malam ba su yafe ba.

Ta yaba halayen malamin inda ta ce ta na alfahari da kasancewa da shi saboda irin kyawawan halayensa.

Ta'aziyyar Gwamna game da rasuwar malamin

Gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya ya mika ta'aziyarsa tare da jan hankalin jama'ar jihar da cewa wannan mutuwa ba ta iyalan malamin kadai ba ne ta jihar ce baki daya.

Don haka ya bukaci kowa ya zama cikin shiri don ba da gudumawa yadda za a dakile wadannan bata gari ba iya jami'an tsaro kadai ba.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta kafa dokar hana fita daga karfe 12:00 na dare zuwa 6:00 na safe, yayin da kakakin rundunar ya tabbatar da cewa su na kan bincike.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Barayi Sun Yi Ajalin Babban Malami A Gombe

A wani labarin, wasu da ake zargin barayi ne sun yi ajalin malamin addinin Musulunci a Gombe, Sheikh Ibrahim Musa (Albanin Kuri) a gidansa da ke Tabra bayan garin Gombe.

Barayin sun yi ajalin malamin ne a daren Talata 8 ga watan Agusta yayin da suka je yin sata a gidan marigayin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel