Buhari Ya Gama Mulki, Amma Yanzu Haka Rayuwar Nadama Yake, Inji Tsohon Ministansa Dalung

Buhari Ya Gama Mulki, Amma Yanzu Haka Rayuwar Nadama Yake, Inji Tsohon Ministansa Dalung

  • Solomon Dalung, tsohon ministan wasanni da ci gaban matasa, ya yi ikirarin cewa, Buhari na cikin nadama saboda yadda mukarrabansa ke bata sunansa
  • A wata hira da aka yi da Dalung, ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawuran da ta daukarwa talakawa a lokacin yakin neman zabe a 2015
  • Duk da sukar da yake yiwa gwamnatin, Dalung na yiwa Buhari kallon shugaba mai gaskiya, inda ya zargi mutanen da ke zagaye dashi da shi da bata masa suna

FCT, Abuja - Tsohon ministan wasanni da ci gaban matasa, Solomon Dalung, ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana rayuwa cikin dana-sani a yanzu haka bayan kammala mulki.

A wata hira da ya yi da gidan rediyon Trust, Dalung ya yi zargin cewa mukarraban Buhari sun ja masa bacin suna da ragin daraja a idon 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Buhari na rayuwa dana-sani, inji Dalung
Dalung ya ce Buhari na rayuwar nadama | Hoto: @viarifnote, @MBuhari
Asali: Twitter

Gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawuran da ta dauka - Dalung

Dalung, wanda ya yi aiki a gwamnatin Buhari, ya kuma yi zargin cewa gwamnatin da ta shude ta kasa cika alkawuran da ta dauka wa Najeriya a lokacin yakin neman zaben 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yana da alhakin fadin gaskiya a matsayinsa na wanda aka kafa jam’iyyar APC mai mulki tare dashi a tun farko.

A kalaman Dalung:

“Mun gaza cimma burinmu, kuma ni ba munafuki bane, domin a matsayina na babban mai ruwa da tsaki da ya yi yakin neman zabe a 2015, na kuma shiga lungu da sako a Arewa, duk alkawuran da muka dauka, ba mu cika ko daya daga cikinsu ba."

Meye alkawuran gwamnatin Buhari?

Ya ce gwamnatin Buhari ta yi alkawarin magance matsalar tsaro, da gyara tattalin arziki, da yaki da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Ruwa Yana Cikin Bacci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

A cewar Dalung:

"Idan muka waiwaya baya, duba da kuma kimanta lamarin a yadda yake a yau, mun gaza sosai."

Buhari shugaba ne mai gaskiya, in ji Dalung

Duk da ganin laifin Buhari wajen cimma burin 'yan Najeriya, Dalung ya bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin shugaba mai gaskiya.

Ya ce mutanen da ke kusa kuma suke kewaye da tsohon shugaban ne suka ja masa bacin suna tare da rage martaba a idon 'yan Najeriya.

Na kusa da Buhari na kange shi da masu fada masa gaskiya

A hirar da muka yi da Dalung a 2021, ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Buhari ke kewaye da mutanen da ba sa fada masa gaskiya.

A hirar, ya bayyana bacin ransa da halin da ake ciki a kasar nan, kama daga batun rashin tsaro har zuwa yadda tattalin arziki ke lalacewa.

A halin da ake ciki, Najeriya na cikin mawuyacin hali, an shiga matsi da matsalolin da suka ninka na mulkin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel