Na kusa da Buhari suna kangeshi da masu fada masa gaskiya, Dalung

Na kusa da Buhari suna kangeshi da masu fada masa gaskiya, Dalung

  • Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya koka kan yadda wasu suka kange shugaba Buhari da masu bashi shawara
  • Dalung ya kuma bayyana ra'ayinsa kan cewa, ba shugaba Buhari ne ya gaza ba, sai dai ba a bashi shawara mai kyau
  • Ya kuma yi kira ga a taya shugaban da addu'ar Allah ya kiyaye shi daga wannan mummunan abu da ya zagayeshi

Abuja - Tsohon ministan wasanni da harkokin matasa, barista Solomon Dalung, ya koka kan yadda wasu makusanta shugaban kasa Muhammadu Buhari a mulki suke kange shi da masu kokarin ganin sun daura shi a turba ta gari da yi wa 'yan kasa hidima.

Dalung ya kuma bayyana cewa, na kusa da shugaban sukan ba da uzurin bogi na cewa, akwai annobar Korona don haka ba za a iya gana wa da shugaban ba.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da wakilinmu a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Ba su yarda mata za su iya jagoranci ba, za mu nuna masu kuskurensu: Shugabar Kasar Tanzania ta magantu

Na kusa da Buhari su suke kangeshi da masu fada masa gaskiya, Solomon Dalung
Barista Solomon Dalung | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yayin da aka tambayeshi game da aikin da na kusa da shugaban ke yi wajen ganin sun wanke Najeriya daga kunya a idon duniya, musamman ta fannin tsaro, Dalung ya bayyana cewa:

"Yana yiwuwa wadanda suke kange shugaban kasa yanzu basa son a bashi wani shawara kan abin da yake faruwa. Kenan, suna niyyar su bashi kunya da rushe kyakkyawar manufa da yake dashi shiyasa suka hana da kange mutane zuwa jikinsa.
"Ai yana zuwa taro, ai yana karbar baki, muna ganin yana karbar mutane, wadannan mutanen basu da Korona ne? ko sai mu da zamu zo mu ganshi ne zamu cutar dashi? "

Ana zargin shugaba Buhari ya gaza wajen magance matsalar tsaro, shin haka ne?

A bangare guda, Dalung ya kuma bayyana yadda mutane da dama ke ganin shugaba Buhari ya gaza wajen inganta tsaro a Najeriya, amma a nasa bangare, ya ce shugaban bai gaza ba sam-sam.

Kara karanta wannan

Abin kunya ne a ce Buhari dan Arewa ne, 'yan Arewa sun soki mulkin Buhari

"Ina ganin kamar matsalar tsaro da aka shiga ciki, wanda 'yan Najeriya suke fama dashi kowacce rana, kuma ana zargin shugaban kasa cewa ya gaza. Ina ganin ba wai lallai ya gaza bane, amma wane irin bayani yake zuwa gareshi?

"Shin abubuwan da suke faruwa yana jin su kamar yadda suke faruwa?
"Amma a nawa tunanin shugaban kasa ya shiga hali na mutane wadanda za su bashi shawara mai kyau sai dai su je kusa dashi su kadai. Wannan a yi addu'a ga Allah, Allah ya taimaki shugaban kasa ya fita cikin wannan hali.

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

A wani labarin, Ganin yadda ake sace yaran makaranta a jihohin Arewacin Najeriya, jaridar Legit.ng Hausa ta yi hira da Solomon Dalung domin jin abin da zai ce.

Da yake magana a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, 2021, tsohon Ministan wasannin da harkokin matasa ya bayyana cewa an shiga tasko a game da sha’anin tsaro.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

Barista Solomon Dalung ya ce da jami’an tsaro sun ga dama, da tuni an ceto wadannan Bayin Allah kamar yadda aka yi ram da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel