Gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawarin da ta yiwa yan Najeriya, Solomon Dalung

Gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawarin da ta yiwa yan Najeriya, Solomon Dalung

- Tsohon ministan Buhari ya caccaki gwamnatinsa kan matsalar tsaro

- Dalung ya ce yanzu shi tsohon dan APC ne amma zai sake rijista

- Matsalar tsaro ya zama babban kalubalen da ake fama da shi a Najeriya

Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya ce gwamnatin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta gaza cika alkawarin da ta yiwa yan Najeriya na magance matsalar tsaro, musamman a Arewa.

Solomon Dalung, wanda ya kasance Minista lokacin wa'adin shugaba Buhari na farko tsakanin 2015 da 2019 ya ce daya daga cikin alkawuran da jam'iyyar tayi shine magance matsalar tsaro, amma ta fadi warwas.

Yayin jawabi a tashar BBC Hausa ranar Asabar, Dalung ya ce mutuncin APC tuni ya zube a idon yan Najeriya, kuma yace babu wanda sake yarda da jam'iyyar.

"Wacce irin gwamnati ne sai mutum ya biya yan bindiga kudi kafin ya iya zuwa gona? Menene rana goben Arewa idan sai ka biya yan bindiga kudi kafin ka samu cika gonarka?", a cewarsa.

"Yanzu zuwa Arewa ya zama abu mai wuya. Matsalar tsaro ya jefa tsoron cikin zukatan al'umma. Kafin mutum ya yi tafiya yanzu sai ya yi addu'a da azumin don ya dawo lafiya."

Ya kara da cewa haka bai taba faruwa a tarihin kasan nan ba.

"Mun yi gwagwarmaya don ganin gwamnatin nan ta hau mulki amma ta gaza amsa bukatunmu. Mun fadawa gwamnatocin baya gaskiya kuma wannan gwamnatinmu ce, wajibi ne mu fadi gaskiya," ya kara.

KU DUBA: COVID-9: Kada ka yi wasa da rayukan mutanenka, Kungiyar NGF ta gargadi wani babban gwamnan Nigeria

Gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawarin da ta yiwa yan Najeriya, Solomon Dalung
Gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawarin da ta yiwa yan Najeriya, Solomon Dalung Hoto: Solomon Dalung Foundation
Source: Facebook

DUBA NAN: Hotuna: Duba gidan da Kamala Harris za ta zauna a matsayin ta na mataimakiyar shugaban Amurka

A bangare guda, Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an raba Naira biliyan 619.343 daga asusun tarayya na FAAC a watan Disamban shekarar da ta wuce, 2020.

Rahoton ya bayyana cewa Naira biliyan 600 ne abin da gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka samu a matsayin kason watan jiya.

Daga cikin wannan kudi, gwamnatin tarayya ta tashi da Naira biliyan 218.3, sannan an raba Naira biliyan 178.3 tsakanin gwamnonin jihohi 36.

Sai kuma kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin Najeriya sun tashi da Naira biliyan 131.8.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel