Yadda Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Da Ke Sharar Bacci Ruwa, Bidiyon Ya Ta Da Kura

Yadda Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Da Ke Sharar Bacci Ruwa, Bidiyon Ya Ta Da Kura

  • Jama'a sun yi cece-kuce a kan wani bidiyo da ke nuna matar aure tana kwararawa mijinta da ke bacci ruwa
  • A cikin bidiyon, mutumin ya tashi a firgice sannan ya fice daga wurin yayin da matar ta dungi yi masa ihu da yarensu
  • Masu amfani da intanet da dama sun caccaki matar kan abun da ta yi wa mijinta sannan sun yi Allah wadai da abun da ta aikata a bidiyon

Wani bidiyo na wata matar aure da ke kwararawa mijinta da ke bacci ruwa ya haifar da zazzafan martani a soshiyal midiya.

Bidiyon wanda @SanphuSA ya wallafa a dandalin X ya yi fice, inda mutane da dama suka yi Allah wadai da abun da matar ta yi.

Matar aure ta kwararawa mijinta ruwa yana cikin bacci
Yadda Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Da Ke Sharar Bacci Ruwa, Bidiyon Ya Ta Da Kura Hoto: @SanphuSA
Asali: Twitter

Kamar yadda @yabaleftonline ta wallafa a dandalin X, matar ta kwararawa malalacin mijinta ruwan dumi ne a jiki. A bidiyon, an gano mutumin da ke bacci a kan kujera ya tashi a firgice bayan an watsa masa ruwan.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Gargadi Yan Mata Da Kyale Saurayinta Da Ya Siya Mota Kwanan Nan, Bidiyon Ya Ta Da Kura

Mutumin ya tashi sannan ya fice daga wajen yayin da ita kuma matar ta ci gaba da masifa da yarensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba a san a ina bane abun ya faru ko dalilin da yasa matar ta aikata wa mijin nata haka.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun caccaki matar kan abun da ta yi wa mijinta

@SasanutritionD ta ce:

"Me yasa yake lalaci? Ya kamata daga maza har mata su kasance masu kwazon aiki don gudanar da harkokinsu na yau da kullun da kuma samun na dogaro da kai."

@only1chiefff said: "Welp.

"Alamu sun nuna mutumin ya gaji sannan ya zabi dan hutawa.
"Na tausaya masa."

@clemzyclemodama ya ce:

"Ina fatan kwa ya ga wannan saboda idan namiji na yi wa mace haka da yanzu abun na yawo a ko'ina."

@ugo_shib ta ce:

"Komai game da shi na nuna lalaci amma a'a kan batun kwatsa ruwan nan fa."

Kara karanta wannan

Namijin Duniya: Wani Dattijo Ya Tsara Budurwa a Waya, Ya Yi Alkawarin Mallaka Mata Zuciyarsa Kacokan

@Ogbovoh90:

"Wannan rashin tausayi ne kuma ba abun yarda bane. Maza na fuskartan abubuwa amma basa magana. Watakila ya aikata ba daidai ba amma wannan ba daidai bane."

Matashiya ta gargadi yan mata kan saurayinta da ya siya mota

A wani labarin, wani bidiyo mai ban dariya na wata mata da ke yawon shakatawa a mota tare da saurayinta ya dauka hankalin mutane a soshiyal midiya.

Matashiya na ta magana a wayarta da kakkausar murya, tana mai jan hankalin yan mata da ka iya kyallara idonsu a kan masoyinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel