Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

  • Salomon Dalung ya na ganin da gangan aka kyale ‘yan bindiga suna ta’adi
  • Tsohon Ministan kasar yace idan an so, za a iya kama masu tada kafar baya
  • Dalung ya yi kira ga shugaban kasa da ya kori duk wanda ya gaza daga ofis

Abuja - Ganin yadda ake sace yaran makaranta a jihohin Arewacin Najeriya, jaridar Legit.ng Hausa ta yi hira da Solomon Dalung domin jin abin da zai ce.

Da yake magana a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, 2021, tsohon Ministan wasannin da harkokin matasa ya bayyana cewa an shiga tasko a game da sha’anin tsaro.

Barista Solomon Dalung ya ce da jami’an tsaro sun ga dama, da tuni an ceto wadannan Bayin Allah kamar yadda aka yi ram da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

“Babu yadda wani zai fada mani jami’an tsaron Najeriya ba za su iya ceto yaran ba, karya ne. Sai dai idan ba su yi niyya.”

Kara karanta wannan

A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

“Idan jami’an tsaron Najeriya za su iya kama jagoran kungiyar da ke fafutukar kasar Biyafara, Nnamdi Kanu, Wallahi Tallahi za su iya kama ‘yan bindiga.”
"Saboda haka ka da a fada mana wani abu dabam. Ba su yi niyya ba, wannan ne gaskiyar. Idan akwai wani abu akasin haka, na kalubalanci shugabanni tsaronmu.”

Dalung da Buhari
Salomon Dalung da Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: pmexpressng.com
Asali: UGC

Salomon Dalung ya yi magana ya na kuka

Yaranmu suna hannun ‘yan bindiga, suna yi mana waya, suna kuka cewa mu kawo kudi ko a kashe su, amma duk da haka Salomon Dalung ya ce an gaza yin komai.

“Ni a matsayina na uba, ina kuka a kowace rana. Yanzu haka da na ke yi maka magana, hawaye ya na zuba a idanu na.”
“Ya ya za a dauke ‘ya ‘yan da muka haifa, a kai su jeji har ana sa masu bindiga a kai, sannan mu na kiran kanmu iyaye, mun gaza yin komai a kansu.”

Kara karanta wannan

Bayan shekara 1 da tunbuke shi, Sanusi II ya fadi abin da ya sa ya zabi ya bar gadon mulki

Allah ya isa!

Salomon Dalung wanda ya na cikin jagororin APC, ya roki jami’an tsaro su rufa wa iyayen wadannan yara asiri, su kubuto da su daga ‘yan bindiga.

Dalung ya hakikance a kan cewa da gangan aka kyale wadannan ‘yan makaranta a hannun ‘yan bindiga

“Abin mamaki, shugaban kasa ya kashe kudi fiye da kowane shugaba a tarihi kan tsaro. Ba ayi kira ba, mai ya ci gawayi. Babu abin da za mu fada sai Allah ya isa.”

Ina mafita?

Dalung ya yi kira ga shugaban kasa ya sauya shugabannin tsaron da suka gaza domin shi za a rika suka a karshe ba wadannan mutane da ya ba mukamai ba.

“Kullum ina addu’a, Allah ya taba zuciyarsa (Buhari), ya dauki gagaruman matakai, ya fita da shi kunya domin ya mika mulki a cikin daraja da mutuncinsa.”

A jiya an ji ‘yan bindigan da su ka yi awon-gaba da Kwamishina a Neja sun tuntubi ‘Yanuwansa. Rahotanni sun ce ana bukatar N500m kafin a fito da Kwamishinan.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya koka kan halin yunwar da al’umma ke ciki, ya ce abubuwa na kara birkicewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel