Hisbah: An Samu Masu Juna Biyu da Kanjamau a Masu Neman Auran Gata a Kano

Hisbah: An Samu Masu Juna Biyu da Kanjamau a Masu Neman Auran Gata a Kano

  • Hukumar Hisbah ta yi bayanin inda aka kwana a shirye-shiryen aurar da marasa karfi a Kano
  • Kakakin rundunar ya bayyana cewa sun ci karo da matan da ke dauke da ciki su na neman miji
  • Da aka yi gwaji a asibitoci, Hisbah ta ce an fahimci akwai masu cututtukan hanta da na kanjamau

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an samu wasu da ke dauke da cututtuka a cikin wadanda ke neman ayi masu auren gata.

Vanguard ta ce cututtukan da aka samu sun hada ciwon hanta na Hepatitis B, sikila da kanjamu.

Mai magana da yawun bakin hukumar ta Hisbah, Lawan Fagge ya ce an gano wannan ne a wajen gwaje-gwajen da ake yi kafin auren.

Hisbah
Shugaban Hisbah, Malam Aminu Daurawa Hoto: Muhammad Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Hisbah ba za tayi aure da ciki ba

Kara karanta wannan

Za a Tsare Mawaka, Naira Marley da Sam Larry na Kwana 21 a Kan Mutuwar Mohbad

Har ila yau akwai matan da aka samu su na dauke da juna biyu a yanzu haka. A musulunci, ba a yin aure dauke da ciki har sai an yi tsarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Lawan Fagge ya ce tuni an maye guraben irin wadannan mutane da aka samu da wasu dabam domin su ci moriyar tsarin gwamnatin.

Hukumar Hisbah za ta taimakawa masu dauke da cututtukan da maganguna, kuma ana basu shawarwarin ganin yadda za su samu lafiya.

Jawabin Kakakin Hukumar Hisbah

"Idan sun samu lafiya, Fagge ya ce nan gaba za a iya aurar da masu dauke da wadannan cututtuka.
Wannan ya na cikin rahoton farko da mu ka samu daga ma’aikatar kiwon lafiya.
Akwai kusan maza da mata 40 da ke da cutar Hepatitis B. Akwai masu cutar sikila, sai kuma masu juna biyu da wadanda ke dauke da kanjamau.

Kara karanta wannan

An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615 da Attajiri Ya Tausayawa Mutanen Kano

Amma a wata mai zuwa za a fara ba su shawarwari kuma a ba su magunguna. Ba a karbe su cikin tsarin ba, amma an maye gurbinsu da wasu.
Za a iya la’akari da su idan sun jurewa shan magunguna kuma sun karbi shawarwarin."

- Malam Lawan Fagge

Da yake jawabi, kakakin na Hisbah ya ce sun tantance masu neman aure kusan 5000, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta aurar da mutane 1800.

Asali: Legit.ng

Online view pixel