Attajiri Ya Tausayawa Mutane a Kano, An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615

Attajiri Ya Tausayawa Mutane a Kano, An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615

  • An samu Attajirin Borno da ya karbi aron gidan mai saboda ya rangwantawa al’umma a Kano
  • Alhaji Ibrahim Jibrin Mohammed ya saida litar man fetur da rangwamen N200 a unguwar Tal’udu
  • Mai kudin ya yi irin wannan taimako a wasu garuruwan, kuma zai cigaba da karya farashin fetur

Kano - Wani Attajiri daga jihar Borno wanda hannunsa a bude yake wajen kyauta, Ibrahim Jibrin Mohammed, ya taimakawa mutane a Kano.

Daily Trust ta ce a ranar Laraba, Alhaji Ibrahim Jibrin Mohammed ya karyawa mutane farashin man fetur, ya saida masu duk lita a kan N415.

Man fetur da mutane su ka saya a kan N615 a gidan man kamfanin NNPCL da ke Tal’udu a Kano, ya koma N415 a sanadiyyar wannan attajiri.

Keke Napep
'Yan Keke Napep na kukan fetur Hoto:thenewshunterblog.wordpress.com
Asali: UGC

Tallafin fetur: Kiran Remi Tinubu ya yi aiki

Kara karanta wannan

An Koma Gidan Jiya, Fetur Ya Fara Wahala, Farashi Ya Haura N650 a Gidajen Mai

Ibrahim Jibrin Mohammed ya ke cewa yayi wannan ne a sakamakon kiran da uwargidar shugaban Najeriya, Remi Tinubu ta yi kwanaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Tinubu ta bukaci mutanen Najeriya su ragewa junansu radadin cire tallafin fetur da aka yi da mai gidanta ya hau mulki a watan Mayu.

Abbakakr Hassan ya wakilci ‘dan kasuwan wajen kaddamar da taimakon, ya ce ya yi haka ne ganin kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ta ke yi.

An saida fetur da araha a Abuja

Ba wannan ne karon farko da ‘dan kasuwan ya yi haka ba, kuma nan gaba za a cigaba da yin hakan a jihohin Kudu maso kudu da na gabas.

"Za mu yi wannan a duka yankunan kasar nan. Mun fara a Maiduguri a Arewa maso gabas, mun yi a Abuja a Arewa maso tsakiya.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Zama Shugaban Najeriya Na Farko Da Kotun Koli Za Ta Tsige – Hadimin Atiku

Yanzu kuma ga mu a Kano a Arewa maso yamma. Za kuma mu yi a Legas (yamma), Fatakwal (Kudu) da kuma Enugu (Gabas)."

- Ibrahim Jibrin Mohammed

Fetur: Gidan mai ya cika

A lokacin da ake saida mai da arahan, rahoton ya ce gidan man ya gamu da cinkoson al’umma.

Wani wanda ya shaida abin da ya faru, ya ce masu babur da motoci sun cika gidan mai, su na neman yadda za sui ya shan man fetur da sauki.

Ana wahalar man fetur

Duk da gwamnatin Bola Tinubu ta janye tsarin tallafin mai, an koma wahalar samun fetur kamar yadda rahoto ya zo mana a cikin makon nan.

Layin motoci da babura sun dawo gidajen mai, farashi ya na cigaba da tashi a kowace rana har ta kai akwai alamun cewa farashi zai iya canzawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng