Mohbad: ‘Yan Sanda Za Su Tsare Mawaka, Naira Marley da Sam Larry na Kwana 21

Mohbad: ‘Yan Sanda Za Su Tsare Mawaka, Naira Marley da Sam Larry na Kwana 21

  • Mutuwar Ilerioluwa Aloba ta jawo ‘yan sanda su na binciken Azeez Fashola da Balogun Eletu
  • Jami’an tsaro sun roki kotu ta ba su damar rike wadannan mutane biyu har na tsawon wata daya
  • Kotu ta yarda a rike taurarin domin bincike, amma ba za su wuce fiye da kwanaki 21 a hannu ba

Lagos - Wata kotun majistare da ke zama a Yaba a jihar Legas ta amince a tsare Azeez Fashola da Balogun Eletu a hannun ‘yan sanda.

Tribune ta ce alkaliyar da ta yi hukunci a ranar Laraba ta ba jami’an tsaro damar rike Naira Marley da Sam Larry domin a iya binciken su.

Domin a kammala duk binciken da ake yi a game da mutuwar mawakin nan, Ilerioluwa Aloba, ‘yan sanda su na bukatar kwanaki 30.

Kara karanta wannan

Wanda Ake Nema Ruwa a Jallo Kan Mutuwar Fitaccen Mawaƙi Ya Miƙa Kansa Ga 'Yan Sanda

B Fig Mohbad Naira Marley Sam Larry
Mohbad, Naira Marley daSam Larry Hoto: @samlarrry/@iammohbad/@nairamarley
Asali: Twitter

Mohbad: 'Yan sanda sun samu kwana 21

Hukuncin mai shari’a Adeola Olatunbosun za ta taimaka domin yin wannan bincike domin gano gaskiyar rasuwar Mohbad a Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya yi aiki da kamfanin Marlian Records wanda Azeez Fashola ya kafa, amma daga baya sai alaka tayi tsami tsakaninsu a bara.

Mutuwar Mohbad ta jawo magana

Shekara guda bayan ya raba jiha da tsohon mai gidansa watau Naira Marley sai kwatsam matashin mawakin ya yi wata mutuwar fuju’a.

Naira Marley da Sam Larry su na cikin wadanda ake zargin su na da hannu a mutuwar Mohbad, zargin da taurarin sun karyata tun tuni.

Rahoton ya ce ‘yan sanda sun gabatar da wadannan mutane biyu a gaban kotun da ke zama Yaba kwanaki bayan an tono gawar mamacin.

Mai shari’a Adeola Olatunbosun ta yarda da bukatar jami’an tsaro, ta ce a tsare mutane biyun da ake tuhuma amma na makonni uku.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Zama Shugaban Najeriya Na Farko Da Kotun Koli Za Ta Tsige – Hadimin Atiku

'Yan sanda na neman Prime Boy

Jaridar This Day ta rahoto SP Benjamin Hundeyin ya na cewa ‘yan sanda su na neman Owodunni Ibrahim wanda ya shahara da Prime Boy.

Bayan sanarwar kakakin ‘yan sandan reshen jihar Legas, sai aka ji Prime Boy ya mika wuya, ya kai kan shi gaban ‘yan sanda a ranar Alhamis.

Shari'a a kan takardun Tinubu

Da bincike ya yi bincike, ku na da labari jami'ar CSU ta nuna akwai alamar tambaya game da takardun kammala karatun shugaba Bola Tinubu.

Jami’ar Amurkan ta ce satifiket din da aka kai wa INEC ya sha bam-bam da wanda ta bada a 1979, Atiku Abubakar ya fake da wannan a kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel