Bidiyon Yadda Matashi Ya Kama Wani Yaro Da Ke Wanke Masa Mota a Boye Ya Yadu

Bidiyon Yadda Matashi Ya Kama Wani Yaro Da Ke Wanke Masa Mota a Boye Ya Yadu

  • Wani dan Najeriya ya lura da kullun motarsa fes-fes take duk cewar mai gadinsa baya wanketa don haka ya yanke shawarar gano bakin zaren
  • Ga mamakinsa wata rana sai ya gano wani yaro yana wanke motar tasa ba tare da ya sanar da kowa ba
  • Mutumin da ya cika da mamaki ya yada bidiyon yaron yana wanke masa mota a boye sannan ya nemi shawarar mutane kan abun da ya kamata ya yi wa yaron

Wani dan Najeriya ya nunawa duniya wani matashin yaro da ke wanke masa motarsa ba tare da saninsa ba.

Mutumin mai suna @koffiseed a TikTok, ya yada bidiyon da ya dauki yaron mai suna Neche cikin sirri a wannan rana, inda ya nemi shawarar mutane kan tukwicin da ya kamata ya ba shi.

Kara karanta wannan

Matashi Na Shirin Yin Wuff Da Dattijuwar Baturiya, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Wani mutum ya kama yaron da ke wanke masa motarsa
Bidiyon Yadda Matashi Ya Kama Wani Yaro Da Ke Wanke Masa Mota a Boye Ya Yadu Hoto: @koffiseed
Asali: TikTok

A cewar mutumin wanda ya kasance Inyamuri, a duk lokacin da ya zo zai yi amfani da motar, ya kan ga an wanke ta kuma ya cika da mamaki lokacin da mai gadinsa ya ce bai san wanda yake wanke ta ba.

Wata rana, sai mai gadinsa ya sanar da shi cewa yaron ya dawo don ya wanke masa motar. Ya ganewa idanunsa lokacin da yaron, matashin da ya sani watanni shida da suka gabata, ya shiga gidan sannan ya fara wanke masa abun hawar tasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Neche ya fadi dalilin da yasa yake wanke motar a sirrince

Ya kira Neche sannan ya yi masa tambayoyi. A cewar Neche, yana aikata hakan ne saboda a gida ba a jan shi a jiki. Ya bayyana cewa yana siyan sabulu da kudinsa ne kuma bai taba damuwa da sanar da mai motar kasancewar bai da waya.

Kara karanta wannan

"Ta Kwanta Da Maza 5": Matashi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ci Amanarsa Daga Tafiya Kasar Waje

Mutumin ya saki yaron don ya ci gaba da wanke motar. Jama'a sun girgiza da wannan halin kirki na yaron.

Kalli bidiyon a kasa:

Karamcin Neche ya tsuma zukata

Mc Talk Talk Udeh ya ce:

"Ban san ka ba faah dan uwa kuma mu ba abokai bane amma ina so na yi masa alkhairi dan kadan."

Andrella ta ce:

"Kuma godiya ga mai gadinka da ya kasance mai gaskiya sannan bai ce shi ya yi abun da ba shi ya yi ba."

Evagold Xclusive Collection ta ce:

"Wayyo Allah ya siya sabulu da kudinsa gaskiya sai da na zubar da hawaye a lokacin da na ga ya fito da sabulu daga aljihunsa."

idk ya ce:

"Tun da har ya wanke motarka sannan ya tafi ba tare da ya nemi a ba shi komai ba ya nuna cewa kai mutuin kirki ne sosai."

Wata uwa ta fashe da dariya ba kakkautawa bayan ganin saurayin diyarta a karon farko

Kara karanta wannan

Namijin Duniya: Saurayi Ya Karbe Shagon Kwantena Da Ya Kerawa Budurwarsa Bayan Ta Rabu Da Shi

A wani labari na daban, wata mai amfani da TikTok mai suna, Angela Mbali, ta tura hoton sahibinta zuwa shafin WhatsApp din yan gidansu don jin ta bakinsu.

Ga mamakinta, mahaifiyarta da kanwarta sun yi martani ga hoton ta hanyar tura sakonnin murya na dariya da nishadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel