“Ta Fara Makaranta”: Yarinyar Da Aka Tsinta a Shara Ta Rayu, Ta Zama Kyakkyawa

“Ta Fara Makaranta”: Yarinyar Da Aka Tsinta a Shara Ta Rayu, Ta Zama Kyakkyawa

  • Karamar yarinyar da wani ya dauka daga inda aka yasar da ita a Enugu ta rayu kuma har ta fara zama cikakkiyar mutum
  • Ben Kingsley Nwashara, ne ya tsinci yarinyar inda ya dunga kula da ita da jin dadinta
  • Yanzu yarinyar ta fara zuwa makaranta, kuma an wallafa sabon hotonta a Twitterm inda ta tsuma zukata da dama

Wani matashi dan Najeriya da ya tsinci yarinya a bola watanni da suka gabata ya yi karin haske kan rayuwar yarinyar.

Bawan Allah mai suna, Ben Kingsley Nwashara, ya tsinci yarinyar da wata da ba a san kowacece ba ta yasar sannan ya dunga kula da ita tun daga lokacin.

Yarinya ta sauya bayan samun kulawa
Yarinyar Da Aka Tsinta a Shara Ta Rayu, Ta Zama Kyakkyawa Hoto: Twitter/@Benking443
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarinyar ta kasance a cikin mugun yanayi lokacin da Kingsley ya tsince ta sannan ya dauke ta zuwa ofishin yan sanda.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Fusata Ta Juye Ruwa a Gadonsu Na Sunna Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashin Kanti

Yarinyar da mahaifiyarta ta jefar da ita ta rayu

Ya bayyana a wata wallafa da ya yi a twitter kwanaki cewa yan sanda basu nuna wani damuwa ba inda suka nemi ya dauke yarinyar daga ofishin yan sandan. Ya ce sai da shugaban yan sandan reshen, DPO ya tsoma baki a wannan rana sannan aka samu maslaha.

Kalamansa:

"A yi hakuri da wannan rubutun. Jami'an yan sanda mata uku ne a bakin aiki a ofishin yan sandan da na kai wannan karamar yarinya a wannan daren. Sun fada mani cewa babu abun da za su iya yi mata kuma cewa na tafi da ita. Dukkansu iyaye ne a ganiyar shekarunsu ta 40. Allah ya sakawa DPO din, Bayarabe da na sama washegari da safe, sannan ya umurci daya daga cikin jami'an mata da ta yi mana rakiya zuwa asibitoci daban-daban mun je can tsawon kwanaki uku don haka suka gan shi a matsayin abun gaggawa sannan suka ba mu kulawa yadda ya kamata. Har ma ya ba mu motarsa da direbansa na tsawon kwana 2."

Kara karanta wannan

Lee Min-ho: Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Dan Koriya, Ya Yi Shigar Kasaita a Wajen Bikinsu

Sabon hoton yarinyar ya nuna cewa an saka ta a makaranta.

Kalli wallafarsa a kasa:Jama

Jama'a sun yi martani yayin da yarinyar da aka tsinta ta fara zuwa makaranta

@PHorpsiey ta ce:

"Shin babu bukatar yin cike-ciken wasu takaudu ko daukar mataki, ko da wani abu na doka zai taso a gaba?"

@philip_george70 ya yi martani:

"Allah ya yi maka albarka Ben. Allah zai ci gaba da kareka da ba ka duk abun da kake bukata don kula da ita."

Alhajin birni ya yi wa budurwa alkawarin miliyan 3 da tafiya hutu waje idan ta boye soyayyarsu

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna @lizzywardrobe_and_jewelsn a TikTok ta bayyana abun da ya wakana tsakaninta da wani alhajin birni.

Ta saki hoton wani sako da ta yi ikirarin alhajin nata ya tura mata ta dandalin WhatsApp.

Asali: Legit.ng

Online view pixel