Wata Uwa Ta Fashe Da Dariyar Keta Bayan Ganin Saurayin Diyarta a Karon Farko

Wata Uwa Ta Fashe Da Dariyar Keta Bayan Ganin Saurayin Diyarta a Karon Farko

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta saki faifan murya da ke nuna martanin mahaifiyarta da kanwarta bayan ganin fuskar sahibinta
  • Matashiyar ta tura hoton saurayin nata zuwa shafin WhatsApp din yan gidansu amma martaninsu ya sa ta jin babu dadi
  • Mutane da dama da suka saurari faifan muryar a TikTok sun shawarci matashiyar da ta kawo karshen soyayyarsu

Wata mai amfani da TikTok mai suna, Angela Mbali, ta tura hoton sahibinta zuwa shafin WhatsApp din yan gidansu don jin ta bakinsu.

Ga mamakinta, mahaifiyarta da kanwarta sun yi martani ga hoton ta hanyar tura sakonnin murya na dariya da nishadi.

Mahaifiyarta ta fashe da dariya bayan ganin hotoin saurayinta
Wata Uwa Ta Fashe Da Dariyar Keta Bayan Ganin Saurayin Diyarta a Karon Farko Hoto: @bigfoots/TikTok.
Asali: TikTok

Sakonnin muryar na kunshe da dariya irin na keta, lamarin da ya jefa Angela cikin rashin tabbass da rashin gane inda suka dosa kan saurayin nata.

Kara karanta wannan

“Allah Ya Sauke Ki Lafiya”: Bidiyon Wata Wada Dauke Da Tsohon Ciki Ya Yadu

Sai dai kuma, duk da dariyar tasu, sun bayyana cewa suna mutunta duk zabin da ta yi wa kanta na wanda take so ya zama abokin rayuwarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsu, idan har tana jin dadi a rayuwar soyayyarsu, shine abun da ya fi muhimmanci a wajensu.

"Idan har kina farin ciki", taken da aka yi wa sakon."

Martanin jama'a yayin da uwa ta fashe da dariya da ganin saurayin diyarta

Mutane sun bayyana cewa idan har yan uwansu suka yi irin wannan martani, toh za su kawo karshen soyayyar ne.

@THABO ta ce:

"Abu kadan aka fadi amma abubuwa da dama hakan ya kunsa."

@The Lady Champagne ta ce:

“Ahhhhh. Shiyasa ba zan iya auren mutumin da ba a tsara shi da kyau ba. Dangina za su yi mun dariya su gaji."

@_jepkemois ta ce:

Kara karanta wannan

Namijin Duniya: Saurayi Ya Karbe Shagon Kwantena Da Ya Kerawa Budurwarsa Bayan Ta Rabu Da Shi

"Na rantse zan rabu da shi nan take."

@Khanyi ta ce:

“Yoh, zan bar dandalin sannan na fice daga duniyar nan."

@kgalalelo ta ce:

"Zan rabu da shi nan take."

Kalli bidiyon a kasa:

Matashi ya karbe shagon kwantenan da ya kerawa budurwa bayan ta rabu da shi

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Amaka Doris, ta ba da labarin yadda tsohon saurayinta, Vene, ya karbe shagon da ya kera mata bayan rabuwarsu.

A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano wata motar daukar kaya dauke da shagon, inda aka bar Amaka cikin mamaki da kunar rai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel