Yadda Tsohon Direban Tasi a Najeriya Ya Siya Mota Kwana 10 Bayan Komawa Kanada

Yadda Tsohon Direban Tasi a Najeriya Ya Siya Mota Kwana 10 Bayan Komawa Kanada

  • Kasa da makonni biyu bayan ya koma Canada, wani dan Najeriya ya yi murnar siyan motarsa ta farko
  • A cewar tsohon direban tasi din, ya siya motar ne a makon da ya fara aiki a kasar ta arewacin Amurka
  • Yayin da mutane da dama ke shakku kan yiwuwar siyar mota a cikin yan kwanaki kalilan da komawarsa kasar, mutumin ya yi karin haske kan yadda lamarin ya faru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mai aikin gini a Najeriya mai suna, @MRBRIKILA1, ya garzaya shafin soshiyal midiya don murnar siyan sabuwar mota kasa da makonni biyu bayan ya koma kasar Kanada.

@MRBRIKILA1 ya wallafa hotunan sabuwar motarsa kirar Honda Odyssey, a shafin X yana mai bayyana cewa ya isa Kanada a ranar Juma'a sannan ya fara aiki a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Dan Adaidaita Sahu Ya Mayar Da Wayar iphone 14 Pro Max Da Fasinjansa Ya Manta Da Shi, Ya Samu Tukwici

Tsohon direban tasi ya siya mota a Canada
Yadda Tsohon Direban Tasi a Najeriya Ya Siya Mota Kwana 10 Bayan Komawa Canda Hoto: @MRBRIKILA1
Asali: Twitter

Yadda ya siya motar

Mutumin, wanda ya yi aiki a matsayin direban tasi lokacin da yake Najeriya, ya ce ya ziyarci wani banci a can don bude asusun ajiya na banki sannan sai manajan ya kira shi bayan ya ga wasikar daukar aikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa manajan ya tambaye shi ko yana da mota sannan ya rubuta masa takardar kudi na dala dubu 5 (sama da miliyan 3.9) na bashi kuma ta kudin ne ya siya mota. Ya rubuta:

"Na isa Kanada a ranar Juma'a...na fara aiki a ranar Litinin da ya biyo baya...
"Na je banki don na bude asusun ajiya.
"Banki ya ga wasikar daukar aikina.
"Manaja ya kira ni, ya tambaye ni ko ina da mota, na ce...yallabai hunturu na zuwa, ya rubuta mun takardar kudi na dala dubu 5 a matsayin bashi.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2 Yayin da Ta Baje Kolinsu a Bidiyo

"Na siyi wannan motar a mako guda.
"Wannan shine fatana gareku dukka...matasan Najeriya da suka kammala NYSC."

Da wasu masu shakku suka far masa, ya tabbatar da labarin, cewa hatta dalibai sun samu katin kudi a ranar da ya suka bude asusu a Canada.

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@QuteWoman ta ce:

"Na tuna lokacin da karfafawa wadanda suka kammala karatu ba aiki gwiwar fara nika timatir da attarugu a kasuwa a matsayin hanyar samun na kai amma Twitter ta dauki dumi."

@ireplazer ya ce:

"A kaddara wannan gaskiya ne, nawa za ka dunga biya kuma tsawon wani lokaci za ka biya. Eh akwai damar samun bashi amma watakila biyan bashi ya dauki tsawon rabin rayuwarka."

@Myckbenny ta ce:

"Ka yi tunani. Za ka dunga daukar fasinjoji a hanyarka na zuwa da dawowa daga aiki.
"Kafin ka sani, ka mayar da kudin da ka siye ta."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mawaki Rarara Ya Gamu Da Tsautsayi Na Hatsarin Mota, Bayanai Sun Fito

Bayan shafe shekaru fiye da 10 a Turai, attajirar da ta koma mahaifarta ta talauce

A wani labari na daban, mun ji cewa wata mata mai suna Beatrice Jockey Mangure ta roki jama'a da su taimaka mata da kudi don ta magance matsalar idonta da kuma fara sana'ar tasi.

Afrimax ya yi hira tare da wallafa labarin Beatrice don sanar da duniya halin da take ciki da nema mata taimako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng