Matashi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ci Amanarsa Da Maza 5

Matashi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ci Amanarsa Da Maza 5

  • Wani ɗan Najeriya ya dawo daga ƙetare ya gano cewa budurwarsa ta ci amanarsa da maza daban-daban
  • Mutumin wanda zuciyarsa ta sosu ya bayyana irin halin da yake ciki a soshiyal midiya inda ya nemi shawarar ya yafe mata ko a'a
  • Masu amfani da yanar gizo sun bayyana ra'ayoyinsu game da halin da mutumin ke ciki tare da bayar da mabambantan shawarwari

Kafin tafiya ƙasar waje, wani ɗan Najeriya ya je an yi musu baiko da budurwarsa domin tabbatar da soyayyar da yake yi mata.

Abin baƙin ciki, da dawowar sa, ya gano cewa ta ci amanarsa inda ta kwanta da maza daban-daban.

Matashi ya kama budurwar da zai aura ta ci amanarsa
Matashin ya rasa abin yi kan laifin da ta yi masa Hoto: Kelvin Murray, Adene Sanchez/ Getty Images (Hotunan an yi amfani da su ne kawai domin misali)
Asali: UGC

Budurwa ta ci yarda ta ci amanar saurayinta

Lokacin da aka tambaye ta, ta yarda cewa ta ci amanarsa da maza da yawa, ta bar shi da zaɓi mai wahala na ko dai ya yafe mata ko ya datse igiyar alaƙar da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Wata Uwa Ta Fashe Da Dariya Ba Kakkautawa Bayan Ganin Saurayin Diyarta a Karo Na Farko, Faifan Muryar Ya Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ina da budurwar da muke soyayya kuma mun amince za mu yi aure kafin in tafi ƙasar waje, amma tace dole na zo na ga iyayenta domin ayi mana baiko kafin na yi tafiyar, domin ta san da gaske nake."
"Bayan na yi wata tara sai na dawo inda na fara zarginta kuma ta tabbatar da cewa ta ci amanata da maza biyar. Yanzu tana ta magiya tana kiran mahaifiyata da ƴan uwanta su roƙe ni na yafe mata, in watsar da ita ko na yafe mata mu cigaba da soyayya? dan Allah a bani shawara na shiga ruɗani."

Masu amfani da yanar gizo sun ba shi shawara

Masu amfani da yanar gizo sun mayar da martani game da halin da yake ciki tare da nasiha mai ban dariya da ke nuna cewa ya kamata ya gafarta wa budurwarsa.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ta Kashe Kudi a Kansa Domin Tafiya Kasar Waje Ya Rabu Da Ita

Ga kaɗan daga ciki nan ƙasa:

@_oyebisi. ta rubuta:

"Ka yafe mata, ka yi ƙoƙari ka tuna da ita a cikin addu'o'inka, ka tuna mata suna son rayuwa da namiji fiye da ɗaya."

@wallpaperplace ya rubuta:

"Maza biyar bayan an muku baiko? Kawu ka je ka tambayi danginta da abin da suka yi maka baiko."

@michael._u ya rubuta:

"Aƙalla ba maza shida ba ne. Idan sun kai shida shi ne sai ka ji haushi. Ka daina wuce gona da iri jor!"

@genny.ngum ta rubuta:

"Ya kamata ya yafe. Bai kamata ya bar gidansa ba wani ya zo ya ji daɗin abin da ya daɗe yana ƙoƙarin ginawa. Bayan haka, cin amanar nan yanzu ya zama ruwan dare."

@ifeomahope2 ta rubuta:

"Don Allah a yi mata addu'a, za ta canza, ka san mace za ta iya cin amanarka kuma tana sonka. Ka taimaka ka yafe mata, sannan ka riƙa ƙoƙarin wanke gajeran wandonka."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Karamar Yarinyar Da Ya Tsinta a Bola, Ta Zama Kyakkyawa Shar Da Ita

Budurwa Ta Shiga Damuwa Kan Saurayi

A wani labarin kuma, wata budurwa ta koka kam yadda saurayin da ta taimaka da kuɗaɗenta domin tafiya ƙasar waje ya manta da ita.

Budurwar ta yi nuni da cewa saurayin na ta na isa ƙasar waje kawai sai ya manta da da ita duk da irin halaccin da ta yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel