Takardun Karatu: Yadda Atiku Yake Shirin Kawo Karshen Bola Tinubu ta Kotun Koli

Takardun Karatu: Yadda Atiku Yake Shirin Kawo Karshen Bola Tinubu ta Kotun Koli

  • Atiku Abubakar ya samu takardun da yake bukata game da karatun Bola Tinubu a jami’ar CSU
  • Lauyoyin ‘dan takaran jam’iyyar hamayyar za su kafa hujja da takardun a shari’ar zaben 2023
  • Burin Atiku shi ne ayi amfani da hujjojin, a ruguza takarar shugaban kasar da Tinubu ya tsaya

Abuja - Ana shari’a tsakanin shugaban Najeriya watau Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar a kan zaben shugaban kasa da aka yi a bana.

Shari’ar zaben ta kai Atiku Abubakar ya lalubo takardun karatun Mai girma Bola Ahmed Tinubu daga jami’ar CSU da ya halarta a Amurka.

Lauyoyin Bola Tinubu sun nemi hana a fito da takardun karatun, amma Mai shari’a Nancy Maldonado ta biya bukatar Wazirin Adamawa.

Tinubu
Digirin Jami'ar CSU Hoto: @DavidHundeyin
Asali: Twitter

Atiku da Tinubu sun sha bam-bam

Kara karanta wannan

Atiku Zai Sheka Kotun Koli da Karfinsa, Jami’ar Amurka Ta Mallaka Masa Takardun Tinubu

Shi dai Shugaba Tinubu ya na ikirarin takardun ba za su yi amfanin komai a kotun koli ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku wanda ya yi wa PDP takara ya na sa ran hujjojin su taimaka masa wajen rusa takarar Tinubu wanda kotu ta ba gaskiya a shari’ar zabe.

Daily Trust ta tattaro takardun da ‘dan takaran PDP a zaben shugaban kasa na 2023 yake so ya yi amfani da su a matsayin hujjoji a gaban koli:

1. Samfurin diflomar da jami’ar CSU ta ba dalibanta a shekarar 1979

2. Takardar shaidar diflomar da aka ba Bola Tinubu a shekarar 1979

3. Takardar shaidar diflomar CSU mai dauke da irin hatimi, sa hannu da rubutun diflomar Bola Tinubu

4. Takardun karatun jami’ar CSU da su ka fito daga hannun babban lauyan makarantar, Jamar Orr.

5. Atiku Abubakar yana so lauyoyinsa su nemi ma’aikatan jami’ar Amurkan su bada shaida a kan ingancin takardun Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Karya ta kare a rikicin takardun Tinubu

Bayan wata da watanni ana fafatawa a kotu, labari ya zo cewa jami’ar CSU ta biyawa Atiku Abubakar bukata, ya samu takardun da yake nema.

Jami’ar jihar Chicago ta fitar da takardun shaidar karatun Bola Tinubu, wanda da su lauyoyin ‘dan takaran PDP za su nemi kafa hujja a kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel