Kotu Ta Amince Da Korafin Atiku Kan Tinubu Dangane Da Jami'ar Chicago Da Shaidar Yin NYSC

Kotu Ta Amince Da Korafin Atiku Kan Tinubu Dangane Da Jami'ar Chicago Da Shaidar Yin NYSC

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar wasu kwararan shaidu a gaban kotun sauraran korafe-korafen zabe
  • Kotun sauraran korafe-korafen zaben da ke zamanta a Abuja ta amince da takardun da mai gabatarwa ya mika a gabanta
  • Jam'iyyar ta gabatar da wannan shaidu ne ta hannun Mike Enahoro Ebah wanda ya gabatar da takardan shaidan aiki da na bautar kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kotun sauraran korafe-korafen zabe a Abuja ta amince da shaidar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar.

Kotun ta karbi wannan takardun ne a ranar Juma'a 23 ga watan Yuni da suka hada da takardar shaidar bautar kasa da na kammala digiri da kuma takardar shaidar aiki na kamfanin Mobil Oil Nigeria Plc.

Kotu ta amince da shaudn da PDP ta gabatar akan Tinubu
Kotun Ta Amince da Shaidun Da PDP ta Gabatar Akan Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Jam'iyyar PDP ta gabatar da shaidar ta hannun Mike Enahoro Ebah wanda ya ce takardun Tinubu ne ya karbe su amma suna dauke da sunan Bola Adekunle Tinubu, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

“Tinubu Ya Nuna Kansa a Matsayin Mace Yayin Neman Gurbin Karatu a Jami’ar Chicago,” Shaidan Atiku Ga Kotu

PDP ta gabatar da shaidu akan Tinubu

Jagoran lauyoyin PDP, Chris Uche ya ce mai ba da shaidan ya kuma gabatar da wasu takardu da kuma wasika zuwa ga hukumar zabe, cewar Legit.ng.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan hukumar zabe, Abubakar Mahmud da lauyan Tinubu, Emmanuel Ukala da kuma lauyan APC, Lateef Fagbemi dukkansu sun ki yarda da wadannan shaidun da PDP ta kawo.

Korafe-korafen da Tinubu ke fama da su tun 1999

Shugaba Tinubu na fama da korafe-korafe tun lokacin da ya zama gwamnan jihar Lagos a shekarar 1999, kamar yadda ICIR A 2022.

Mafi yawan korafe-korafen sun hada da hanyar arzikinsa da rashin lafiya da kuma zargin cin hanci.

Sauran sun hada da zargin safarar kwayoyi da mallakar takardun bogi da sauransu.

Bayan Tinubu Ya Shiga Ofis, Atiku Da Obi Sun Cigaba Da Shirin Karbe Mulki A Kotu

Kara karanta wannan

Sabon ‘Dan Majalisa Ya Fara Yi wa Mutanen Mazabarsa Alheri Daga Rantsar da Shi

A wani labarin, an gano dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shiga kotu da tulun takardu don kalubalantar zabe.

Atiku da jam'iyyar PDP sun shigar kara kan zargin magudin zabe da aka tafka a zaben da ya gabata.

Peter Obi da Atiku Abubakar na kalubalantar babban zaben da aka gudanar a watan Faburairu na shugaban kasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel