Yajin Aiki: Gwamnatin Tinubu Ta Sake Gayyatar Kungiyoyin Kwadago

Yajin Aiki: Gwamnatin Tinubu Ta Sake Gayyatar Kungiyoyin Kwadago

  • Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Tinubu ta gayyaci shugabannin kungiyoyin kwadago domin wani taron tattaunawa a ranar Lahadi
  • Taron dai za a yi shi ne domin daƙile yajin aikin sai baba-ta-gani da shugabannin ƙungiyoyin kwadagon da suka haɗa da NLC da TUC suka shirya farawa
  • A cewar sanarwar da ta fito daga ma'aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, taron zai gudana ne a ɗakin taro na shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta sake yin wani yunkuri na dakatar da yajin aikin da kungiyoyin kwadago ke shirin yi a fadin ƙasar nan, yayin da gwamnati ta gayyaci shugabannin kungiyar domin sake tattaunawa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, za a gudanar da taron ne ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, da misalin ƙarfe 2:00 na rana fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Dama-dama: Tinubu ya karawa ma'aikata albashi, amma akwai abin kura a gaba

FG ta sake gayyatar kungiyoyin kwadago
Gwamnatin tarayya ta sake gayyatar kungiyoyin kwadago domin tattaunawa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu zai sake yin wani taro da NLC

A ranar Juma'a 29 ga watan Satumba ne gwamnatin tarayya ta shirya wani taro da kungiyoyin kwadago, amma shugabannin kungiyar ba su halarta ba, kuma taron bai yiwu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata takarda da wani darakta a ma'aikatar ƙwadago, Emmanuel Igbinosun, ya fitar a madadin ministan, ya mika wa shugaban kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), an gayyaci shugabannin kungiyar taro a fadar shugaban ƙasa a ranar Lahadi.

Shugabannin ƙungiyoyin da ake sa ran gani a taron sun hada da wakilai da shugabannin ƙungiyar NLC da takwarorinta na ƙungiyar ƴan kasuwa ta ƙasa (TUC).

Gbajabiamila, Lalong, za su tattaunawa da NLC, TUC

Wakilan gwamnati da ake sa ran za su halarci taron su ne shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ministan ƙwadago da samar da ayyuka, Simon Lalong, Nkiruka Onyejeocha, ƙaramar ministan ƙwadago, da sauran manyan jami'an gwamnati.

Kara karanta wannan

Saura kiris: Tinubu ya ce a kara hakuri, yana kan hada yadda zai ragewa 'yan kasa shan wahala

NLC Ta Magantu Kan Kin Halartar Taro Da FG

A wani labarin kuma, ƙungiyar ƙwadago ta bayyana dalilin da ya sanya ba ta halarci taron da gwamnatin tarayya ta gayyace ta ba kan yajin aikin da take shirin farawa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ba a sanar da ita taron a kan lokaci ba ne shiyasa ba ta amsa gayyatar da gwamnatin tarayyar ta yi mata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel