Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Dalilin Kin Halartar Taro Da FG

Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Dalilin Kin Halartar Taro Da FG

  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun bayyana dalilin da ya sanya ba su halarcci taron da gwamnatin tarayya ta kira su ba
  • Kingiyoyin sun bayyana cewa gwamnatin ba ta aike musu da takardar sanarwar taron ba a kan lokaci
  • Ƙungiyoyin ƙwadagon dai na shirin fara yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin ƙasar nan a ranar, 3 ga watan Oktoba

FCT, Abuja - Gabanin fara yajin aikin da ƙungiyoyin kwadago suke shirin yi a ranar 3 ga watan Oktoba, taron da gwamnatin tarayya ta kira tare da shugabannin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), da ƙungiyar ƴan kasuwa ta kasa (TUC), bai yiwu ba.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa taron bai yiwu ba ne sakamakon sanarwar da aka bayar cikin taƙaitaccen lokaci.

Kungiyar kwadago ta fadi dalilin kin halartar taro da FG
Kungiyar ta ce ba a sanar da ita kan lokaci dangane da taron Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya ta gayyaci shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon biyu domin yin wani taro a ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasa ta Villa a Abuja, kan yajin aikin da suke shirin farawa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Bayan Yan Bindiga Sun Kona Gidan Babban Dan Majalisa a Najeriya

Sai dai, taron bai gudana ba saboda da yawa daga cikin shugabannin ƙungiyar sun bar Abuja kafin a karɓi takardar gayyatar taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƙungiyoyin ƙwadago ƙin halartar taron?

Wata majiya mai tushe ta daga ƙungiyar kwadagon ta bayyana cewa sanarwar taron da ta fito daga ma'aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, ta samu ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Juma'a, lokacin bai fi saura sa'o'i biyu a fara taron ba kamar yadda aka tsara.

A cewar majiyar:

"Mun samu sanarwar taron ne da misalin karfe 10 na safe kuma an shirya gudanar da taron a fadar gwamnati da ƙarfe 12:00 na rana. A lokacin da muka samu gayyatar, yawancin shugabannin sun bar Abuja domin zuwa jihohinsu."
"Ina ganin gwamnati ba ta shirya ganawa da mu ba. Ta yaya za ku sanya taro da ƙarfe 12:00 na rana kuma ku aika gayyata ko sanarwar taron da ƙarfe 10:00 na safe, kusan sa'o'i biyu kafin lokacin da aka tsara?"

Kara karanta wannan

Diyyar N30bn: Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotu, Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka

"Ba za mu iya ƙin tattaunawa da gwamnati ba, amma ba mu ga wani abu wanda ya nuna cewa da gaske gwamnati take ba, illa kawai barazana, ɓatanci da ɗaukar nauyin ƙungiyoyi su soki ƙungiyar ƙwadago."

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, babu wani bayani kan ko gwamnati na shirin sake sanya wani lokaci domin gudanar da taron ko a'a.

Kungiyoyin Kwadago Za Su Shiga Yajin Aiki

A baya rahoto ya zo cewa ƙungiyoyin ƙwadago sun shirya shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin ƙasar nan.

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun sanar da cewa za su fara yajin aikin ne a ranar 3 ga watan Oktoban 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel