Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Najeriya

Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Najeriya

  • Ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa NLC da TUC sun tabbatar da shirinsu na gurgunta tattalin arziƙin Najeriya da yajin aiki
  • A wani taron manema labarai a Abuja, ƙungiyoyin sun ayyana shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 3 ga watan Oktoba, 2023
  • Sun ɗauki wannan matakin bayan gazawar gwamnati na cika musu buƙatunsu sakamakon cire tallafin man fetur

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Manyan ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC zasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a faɗin Najeriya daga ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, 2023.

Shugabannin ƙungiyoyin NLC da TUC ne suka sanar da haka a wani taron manema labarai da suka kira a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata (yau) 26 ga watan Satumba, 2023.

NLC da TUC sun sanar da tsunduma yajin aiki a Najeriya.
Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Najeriya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa ƙungiyoyin sun umarci rassansu na jihohin Najeriya su rufe harkokin tattalin arziƙi daga ranar Talata ta mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Hana Majalisa Tsige Mataimakin Gwamnan APC, Ta Bayyana Dalilanta

Bayan haka kuma sun buƙaci kowane reshen ƙungiyoyin ya fara shirin fita zanga-zangar lumana a dukkan sassan ƙasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NLC da TUC sun warware saɓaninsu

Channels TV ta tattaro cewa shugabannin kwadagon biyu sun warware sabanin da ke tsakaninsu wanda ya sa NLC ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu ba tare da TUC ba.

A cewar sanarwar taron mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar NLC, Emmanuel Ugboaja, taron ya gudana ne ta hanyar amfani da fasahar zamani.

FG ta roƙi NLC da ƙara hakuri

A halin da ake ciki, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ya roki shugabannin NLC da su janye yajin aikin da suke shirin fara wa a ƙasar nan.

Ya tabbatar musu da cewa gwamnatin tarayya ta shirya magance musu dukkan damuwar da suka gabatar cikin kanƙanin lokaci.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Ministan ya ce ɗaya daga cikin manyan bukatun kungiyar NLC a taron da suka yi na ƙarshe an cika musu shi, wanda ke da alaka da sakin shugabannin kungiyar ma’aikatan sufuri ta Najeriya (NURTW).

Kotu Ta Kori Karar PDP da Sandy Onor Kan Zaben Gwamnan Jihar Cross River

A wani rahoton kuma Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna ta yanke hukunci kan nasarar gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu.

Kwamitin alkalan Kotun, yayin yanke hukunci ranar Talata, ya kori.ƙarar jam'iyyar PDP da ɗan takararta bisa rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel