Jerin Fastocin Da Suka Hango Za a Cafke Peter Obi a Watan Satumba

Jerin Fastocin Da Suka Hango Za a Cafke Peter Obi a Watan Satumba

Fastoci da dama sun yi hasashen cewa hukumomi za su kama Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairun 2023, gabanin sauraron ɗaukaka ƙarar da ya yi a kotun ƙoli.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A watan Satumba kaɗai, aƙalla fastoci biyu sun yi ikirarin cewa sun hango wahayin yadda za a cafke tsohon gwamnan jihar Anambra.

Fastoci sun yi hasashen za a cafke Peter Obi
Fastocin sun yi hasashen cewa hukumomi za su yi caraf da Peter Obi Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Peter Obi ya ƙalubalanci nasarar Tinubu a kotu

Obi da jam’iyyar Labour ne suka zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Sun shigar da ƙara ne akan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta yi.

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) ta yi watsi da koke-kokensa kan rashin samun hujjoji.

Kara karanta wannan

Gobara Ta Laƙume Takardun Ƙarar Zaben Shugaban Ƙasa a Kotun Ƙoli? Gaskiya Ta Bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da da yawa ke jiran hukuncin kotun ƙolin, wasu fastoci sun yi hasashen cewa za a cafke ɗan takarar shugaban ƙasan cikin ƙanƙanin lokaci.

Ga jerinsu a nan ƙasa:

Fasto Dauda Kingleo Elijah

A cikin wa'azinsa na kwananan nan, faston wanda yake a jihar Legas, ya ce ya hango an yi wa Peter Obi ɗaurin talala.

A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na YouTube, faston ya yi kira ga magoya bayan tsohon gwamnan na jihar Anambra da aka fi sani da 'Obidients' da su yi wa ɗan takararsu addu'a da kada a tsare shi a gidan yari.

A kalamansa:

"Dole ne ku yi wa ɗan uwanku, ɗan takararku, Peter Obi addu'a, ku yi masa addu'a, domin ban san me ake nufi da wannan ɗaurin talalan ba, menene laifin? Me ya faru? Ban sani ba."

Kara karanta wannan

Reno Omokri Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Legas

Fasto Elijah Bamidele

Shugaban cocin Christ House of Prayer and Deliverance Ministry, Legas, ya ce ya gani a cikin wahayinsa cewa an kama Peter Obi kuma an sanya masa ankwa.

A kalamansa:

"Na ga an sanya wa Peter Obi ankwa."
"Wannan ita ce shawarata ga Peter Obi. Ka bi a hankali. Domin na gani, ko in kira shi da taron dangi. Na gan shi tsare a hannun DSS. Don kada lamarinsa ya zarce na Mazi Nnamdi Kanu muni, na ga hakan a bayyane."

Fasto Ya Yi Hasashen Abin Da Atiku/ Obi Za Su Tarar a Kotu

A wani labarin na daban kuma, fasto Elijah Ayodele, ya bayyana abin da ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun Labour Party da PDP, Peter Obi da Atiku Abubakar, za su tarar a kotun ƙoli.

Fasto Ayodele ya bayanin cewa Obi da Atiku ƙuɗinsu kawai za su ɓarnatar ta hanyar zuwa kotun ƙolin saboda ba za su iya sanya wa a soke nasarar da Shugaba Tinubu ya samu ya zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel