Mun Gaji Da Irin Alkawuran Karya Na Shugaba Tinubu, Kungiyar TUC

Mun Gaji Da Irin Alkawuran Karya Na Shugaba Tinubu, Kungiyar TUC

  • Kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC ta ce ta gaji da yadda Tinubu ke musu alkawura da ba ya cika musu
  • Shugaban kungiyar, Festus Osifo shi ya bayyana haka a yau Talata 26 ga watan Satumba yayin hira da gidan talabijin na Channels
  • Ministan kwadago da ayyuka, Simon Lalong a baya ya yi wa kungiyoyin alkawarin cewa za a dauki mataki kan matsalar

FCT, Abuja – Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa (TUC) Festus Osifo ya bayyana cewa kungiyarsu ta gaji da karerayin Gwamnatin Tarayya.

TUC na bukatar tallafawa ma’aikata don rage musu radadin cire tallafi da su ke ciki da cire biyan haraji ga wasu ma’aikatan da kuma tsara rabon kayan tallafi.

Kungiyar TUC ta ce ta gaji da alkawuran karya na Tinubu
Mun Gaji Da Irin Alkawuranka, Kungiyar TUC Ga Tinubu. Hoto: Festus Osifo, Bola Tinubu, Joe Ajaero.
Asali: Twitter

Meye kungiyar TUC ke cewa kan Tinubu?

Kungiyar ta ce a kullum ma’aikatar ayyuka da kwadago na musu alkawura amma ko daya daga ciki ba su iya cika ba, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan kwadago da ayyuka, Simon Lalong a baya ya yi alkawari ga ma’aikatan cewa za a duba yiyuwar yI musu wani abu kan albashinsu.

Ministan ya kuma roki kungiyar kwadago ta NLC da kada ta tsunduma yajin aiki inda ya yi alkawarin daukar mataki daga gwamnati.

A wata hira da 'yan jaridu a yau Talata 26 ga watan Satumba a Abuja, Osifo ya ce su na bukatar daukar matakin gaggawa kan matsalolinsu, Within Nigeria ta tattaro.

Wane sako TUC ta turawa Tinubu?

Ya ce:

“A ganawa da mu ka yi ta karshe, ma’aikatar kwadago da ayyuka ta mana alkawari cewa da zarar Shugaba Tinubu ya dawo zai yi bayani kan matsalar.
“Da safen nan ma sun sake cewa za a shawo kan matsalar nan ba da jimawa ba, mun gaji da nan ba da jimawa ba, mu na bukatar matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ware Naira Dubu 245 Ga Ko Wane Mai Bautar Kasa, Ya Yi Alkwari Ga Wasu Matasan

“A karshe, mu na ta jin ana sa kwanan wata ace yau ko gobe ko jibi, mun gaji da jin haka, abin da mu ke so kawai shi ne daukar mataki.”

Osifo ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun gaji da yawan ganawa da kungiyaoyin ke yi da Gwamnatin Tarayya.

Ya ce a gaskiya sun gaji da alkawura da gwamnatin ke yi musu a duk lokacin da su ke ganawa.

Abin da Tinubu ya fada mana kan albashin ma'aikata

A wani labarin, shugaban kungiyar kwadago (TUC) Festus Osifo ya bayyana abinda Bola Tinubu ya fada musu a ganawar da su ka yi.

Kungiyar ta bai wa gwamnati tsawon makwanni da ta magance matsalolin da ake ciki sakamakon cire tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel