Tinubu Ya Sake Karbo Bashin $700m Daga Bankin Duniya, Na Uku Tun Bayan Da Ya Zama Shugaban Kasa

Tinubu Ya Sake Karbo Bashin $700m Daga Bankin Duniya, Na Uku Tun Bayan Da Ya Zama Shugaban Kasa

  • Gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake karbo bashi daga babban bankin duniya
  • Bashi ya kai kimanin dala miliyan 700 kuma zai taimakawa shirye-shiryen gwamnatin Najeriya na ilimi, musamman kan yara mata
  • Sabon bashin shine irinsa ba uku da shugaban kasa Tinubu ke karbowa tun bayan da ya hau mulki

Gwamnatin tarayya ta sake ciyo sabon bashi na dala miliyan 700 daga bankin duniya, na uku da ake amincewa da shi a karkashin gwamnatin Bola Tinubu.

An amince da na farkon a ranar 9 ga watan Yuni, inda aka bayar da bashin dala miliyan 500 domin bunkasa ma'aikatar wutar lantarki na Najeriya.

Tinubu ya sake samo bashin dala miliyan 700 daga bankin duniya
Tinubu Ya Sake Karbo Bashin $700m Daga Bankin Duniya, Na Uku Tun Bayan Da Ya Zama Shugaban Kasa Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Facebook

Na biyun ya kasance bashin dala miliyan 500 domin taimakawa Najeriya wajen tallafawa mata, kuma an amince da shi a ranar 22 ga watan Yunin 2023, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Wa 'Yan Najeriya Babban Alkawari Guda 1, Ya Ce Ko Za A Tsane Shi Sai Ya Gyara Kasar

Bayanai kan sabon bashi

An sanar da sabon bashin ne a cikin wata sanarwa da bankin duniyan ya fitar a shafinsa na yanar gizo a ranar Juma'a, 22 ga watan Satumbar 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, bashin dala miliyan 700 din zai bunkasa ilimi da tallafawa yara mata.

Hakazalika, an karbi sabon bashin ne don samar da karin kudi saboda wani aiki da ke gudana na Shirin Bunkasa Ilmin yaya Mata wato AGILE.

Sanarwar ta ce:

“Bankin Duniya ya amince da karin tallafin dala miliyan 700 ga Najeriya don bunkasa Shirin Bunkasa Ilmin yaya Mata wanda manufarsa shi ne inganta damar samun ilimin sakandare a tsakanin yara mata a wasu jihohi.
"Karin kudin zai habaka ayyuka daga jihohi bakwai da ake kai a yanzu zuwa karin jihohi goma sha daya da kuma kara yawan masu cin gajiyar shirin don shigar da yara mata da suka bar makaranta, masu aure, da masu bukata ta musamman."

Kara karanta wannan

China Ta Rage Yawan Bai Wa Najeriya Bashi Kan Dalili Daya Tak, Ta Bayyana Dalilin Matakin

Jihohi bakwai da aka aiwatar da shirin AGILE sune Borno, Ekiti, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, da Plateau.

Bankin duniya na ganin sabon kudin zai bunkasa shirin zuwa jihohi 18 da kuma taimakawa Najeriya wajen samawa yara mata ingantacciyar ilimi da kiwon lafiya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, baya ga yan matan da za su ci gajiyar tallafin, sauran da za su amfana sun hada da dalibai sama da miliyan 15 da wadanda suka amfana, kamar su malamai, masu gudanarwa, iyalai, al’umma, da ma’aikata a makarantu.

China ta rage yawan basukan da ta ke bai wa Najeriya da sauran kasashe saboda saba doka

A wani labari na daban, mun ji cewa yawan bashin da kasar Sin da ta ke bai wa Nahiyar Afirka ya ragu zuwa Dala biliyan daya a shekarar da ta wuce mafi karanci kenan cikin shekaru 20.

Wannan na zuwa ne yayin da mafi yawan kasashen Nahiyar Afirka su ka gagara cika umarnin biyan bashin, cewar Reuters.

Asali: Legit.ng

Online view pixel