Dangote Ya Sake Hayewa Teburin Masu Kudin Nahiyar Afirka Bayan Samun Ribar Naira Biliyan 13 A Sa'o'i 24

Dangote Ya Sake Hayewa Teburin Masu Kudin Nahiyar Afirka Bayan Samun Ribar Naira Biliyan 13 A Sa'o'i 24

  • Alhaji Aliko Dangote ya sake karbar matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka bayan ture dan kasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert
  • Dangote ya samu tagomashin ne bayan samun karuwar fiye da Naira biliyan 13 a cikin sa'o'i 24 kacal a yau Litinin
  • Duk yawan kudin da Dangote ke da shi, har yanzu ya na kasa da Dala biliyan 11 dadi da kari kuma kullum farashin Naira faduwa ta ke

FCT, Abuja - Alhaji Aliko Dangote ya sake karbar matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka bayan doke Johann Rupert.

Dangote ya koma mataki na daya wata daya bayan ya rasa matsayin kan sabbin tsare-tsare na Babban Bankin Najeriya, CBN.

Dangote ya karbi matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka
Yanayin Yadda Taswirar Kudin Dangote Ke Sauka Da Tashi. Hoto: Forbes.
Asali: Facebook

Nawa Dangote ya mallaka a yanzu?

Attajirin ya dawo na biyu a kwanakin baya yayin da dan kasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ya haye matakin farko, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: An Fadawa Tinubu Abu Daya Tak Da Zai Yi Don Shawo Kan Matsalar Tsaro A Jihar Arewa, Ta Nemi Bukata

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mujallar Forbes ta fitar da sanarwar cewa a yanzu Dangote na da kudi har Dala biliyan 10.9 a yau Litinin 14 ga watan Yuli.

Hakan ya dara na Johann Rupert da ya ke da Dala biliyan 10.8 zuwa yau Litinin 14 ga watan Agusta.

Mujallar ta kara da cewa Dangote ya kara sama da mataki daya a masu kudin duniya a matsayi na 166.

Yayin da mai binsa a mataki na biyu a Afirka ke matsayi na 167 a duniya.

inda Dangote yafi samun kudadensa shi ne kamfanin siminti da kuma kamfanin sukari sai kuma hannun jari a bankin UBA.

Shin Dangote zai iya ci gaba da rike kambun?

Ana sa ran duk ranar da matatar mai din attajirin ta fara aiki da cire gangan mai 650,000 a rana, arzikinsa zai ninku.

Kara karanta wannan

Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Ambato Kuskuren Da Shugaba Tinubu Ya Fara Daga Hawa Mulki

Sauran mashahuran masu arziki a Najeriya sun hada da:

1. Abdussamad Rabiu - Dala biliyan 5.6

2. Mike Adenuga - Dala biliyan 3.6

Dangote Ya Yi Asarar Naira Biliyan 480 A Sa'o'i 24

A wani labarin, Aliko Dangote ya yi asarar fiye da Naira biliyan 184 a cikin sa'o'i 24 kacal.

Dangote dai shi ne ke mataki na biyu a Nahiyar Afirka bayan dan Afirka ta Kudu ya doke shi a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel