Dangote Ya Tafka Asarar N480bn A Cikin Sa’o’i 24, Ya Rasa Matakin Farko A Afirka

Dangote Ya Tafka Asarar N480bn A Cikin Sa’o’i 24, Ya Rasa Matakin Farko A Afirka

  • Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya samu tasgaro a harkokin kasuwancinsa bayan tafka asara da ya yi cikin sa'o'i 24
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Dangote ya yi asarar Naira biliyan 483.87 ko wane minti a cikin sa’o’i 24 da suka wuce
  • Wannan na zuwa ne bayan biloniyan ya rasa matakin mafi kudi a Nahiyar Afirka inda Johann Rupert na Afirka ta Kudu ya sha masa kai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Alhaji Aliko Dangote, mamallakin kamfanonin Dangote a Najeriya ya yi asarar Dala miliyan 613 kwatankwacin Naira biliyan 483.87 cikin ko wane minti daya a sa’o’i 24.

Mujallar Forbes ta wallafa cewa Dangote yanzu ya dawo kasa da mallakar kudi Dala biliyan 10.5 a rahoton da ta fitar yau Laraba 9 ga watan Agusta, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sanatan NNPP Zai Kashe Fiye da N20m Wajen Biyawa Dalibai Kudin Karatu a Kano

Dangote ya yi asarar Naira biliyan 480 a ko wane minti daya cikin sa'o'i 24
Asarar Da Aliko Dangote Ya Tafka Ta Kai N480bn A Cikin Sa’o’i 24. Hoto: Tekedia.
Asali: UGC

A mataki na nawa Dangote ya ke?

Hakan shi ya sanya Dangote a mataki na biyu cikin jerin masu kudin Nahiyar Afirka wanda dan kasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ya mallaki kudi Dala biliyan 10.9.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mujallar Forbes ta kuma tabbatar da cewa Aliko Dangote a yanzu ya na mataki na 176 a jerin masu kudin duniya.

Tun bayan ba da damar Naira ta yi yawo da Babban Bankin Najeriya (CBN) ta yi a hada-hadar kudade a kasuwa, Dangote ke samun asasrar biliyoyi da ke ruguza masa arziki.

Nawa Dangote ya mallaka a farkon shekara?

Hakan bai rasa nasaba da cewa kusan dukkan harkokin kasuwanci da Dangote ya ke yi su na da alaka da Naira, cewar Tribune.

Rahotanni sun tabbatar cewa a farkon wannan shekara, Dangote ya mallaki kudi da ya kai Dala biliyan 12.5 yayin da ya sake sama da Dala biliyan 14 a watan Faburairu na 2023.

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna Ya Jagoranci Jami’an Tsaro An Dura Gungun ‘Yan ta’adda Cikin Dare

Labarin ya sauya tun bayan tsare-tsare da babban bankin kasar ta kawo na barin Naira ta yi yawo da sauran sauye-sauye na Gwamnatin Tarayya.

Kamfanonin Simintin Dangote Da BUA Sun Kashe Kudi N205bn Kan Siyan Fetur Cikin Watanni 6

A wani labarin, kamfanonin siminti na Dangote da BUA sun bayyana biliyoyin Nairori da su ka kashe cikin watanni shida kan man fetur.

Kamfanonin su ka ce sun kashe a kalla Naira biliyan 205 a cikin wannan shekara a watanni shida kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.