Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Bi Titi Tana Rokon a Hada Mata Kudin Siyan iPhone 15 Ya Ba da Mamaki

Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Bi Titi Tana Rokon a Hada Mata Kudin Siyan iPhone 15 Ya Ba da Mamaki

  • Wata mata da ta kirkiri wata hanya don tara kudi don nemawa wani dan Najeriya taimako ta fito tana neman a tara mata kudin siyan waya iPhone 15
  • Da yawan masu wucewa sun yi mamakin lamarin yayin da wasu ke ba ta dan abin da suke da shi a matsayin tallafin siyan waya
  • Matar ta ta tattara dukkan kudin da ta tara a rana ta ba wani lebura bias ganin gwazonsa da yadda yake aiki tukuru

Wata kyakkyawar mata ‘yar Najeriya ta bai wa mutane da dama mamaki lokacin da ta dauki kwali da ke dauke da kalmonin rokon kudin siyan waya iPhone 15.

Mutane da yawa da suka ganta a titi tana neman kudin da za ta sayi waya iPhone 15 sun yi mamaki kuma ba su boye yadda suka ji game da matakin nata ba.

Kara karanta wannan

Hotunan Wani Katafaren Gida Da Za a Siyar Miliyan 1.5 Ya Girgiza Intanet

Matar mai suna @meyiwa_vera bata tsaya raina kyauta ba, kana bata tsaya wasa ba a lokacin da mutane suka fara ba ta kudi don cika burinta.

Yadda wata ke neman kudin siyan iPhone
iPhone ta nemi saya, ta kyautar da kudin | Hoto: @meyiwa_vera
Asali: TikTok

Sai dai, abin da ya ba mutane mamaki shi ne, a karshen bidiyon an ga yadda ta dauki dukkan kudaden da ta tara ta ba wani lebura, lamarin da ya ja hankalin mutane da dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a nan:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

A bangare guda, mutane da yawa sun bayyana martani mai daukar hankali game da abin da wannan matar ta aikata mai taba zuciya. Ga kadan daga abin da suke cewa:

CLASSIC TORY:

“Kenan mai buga bulo ne ya cinye kudin siyan iPhone 15 din.”

Thic Cinderella:

“Farko na yi tunanin da gaske roko take don ta siya iPhone 15... Allah ya miki albarka.”

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Saurayi Ya Yi Mata Korar Kare Daga Gidansa a Bidiyo

Bolarinwa:

“Kawai ka zama na kirki wani zai ce ni da ban taba amfani da iPhone 14 ba a baya, amma ki za ki sayi iPhone 15 amma dai ka zama na kirki.”

Deeyor stanley:

“Ina fatan dai duk da haka kin sayi iPhone 15 din.”

heyyyitsKemiron baby:

“Karshe kenan. Ina son ganin karshen yadda ake kayawa da wasan banza a karshe.”

anyadikegoodness:

“Ina jin bani da kudi abin da zan yi kenan.”

Yadda mai iPhone da Samsung suka yi gasa

A wani labarin, wani matashi, @her.ex_boyfriend,_, da abokansa sun dauki hankulan mutane da dama yayin da suka saka wayoyinsu na iPhone 14 pro max, iPhone 13 pro max, da Samsung S22 a cikin mazabi da ruwa.

Mutumin da ya wallafa bidiyon ya ce suna son su gwada wacce cikin wayoyin ta fi karko a bangaren jure ruwa.

Bayan sun saka wayoyinsu masu tsada a cikin ruwa, sun yi amfani da agogo sun saka lokaci. Bayan minti daya, wayoyin iPhone din sun dauke wuta.

Kara karanta wannan

“Rabona Da Wanka Shekara 1”: Yar Najeriya Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo, Tana Neman Agaji

Asali: Legit.ng

Online view pixel