Matashin Da Ya Siyawa Budurwarsa Sabon iphone 15 Ya Zauce Bayan Ya Samu Sakon Sai Wata Rana

Matashin Da Ya Siyawa Budurwarsa Sabon iphone 15 Ya Zauce Bayan Ya Samu Sakon Sai Wata Rana

  • Wata budurwa yar Najeriya ta nunawa duniya martanin saurayinta bayan ta zolaye shi da sakon rabuwa na bazata
  • Saurayin ya aika sakon murya yana mai nuna rashin yarda da takaicinsa kan shawarar da budurwarsa ta yanke na kawo karshen soyayyarsu
  • Sakon muryar ya bai wa mutane dariya sannan sun garzaya sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu game da shi

Wata matashiya yar Najeriya mai suna @graciajoliee a TikTok ta yi fice bayan ta zolayi saurayinta da sakon rabuwa.

Matashiyar ta kadu yayin da saurayin nata ya amsa mata da sakon murna yana mai nuna rudani da takaicinsa.

Budurwa ta zolayi saurayi da sakon rabuwa
Matashin Da Ya Siyawa Budurwarsa Sabon iphone 15 Ya Zauce Bayan Ya Samu Sakon Rabuwa Sai Wata Rana Hoto: @graciajoliee/TikTok.
Asali: TikTok

Martanin saurayi kan sakon rabuwa na bazata

A cikin sakon muryar, saurayin ya tambayi dalilinta na son kawo karshen soyayyarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bayan Shekara 7 Suna Soyayya, Budurwa Ta Yi Wuff Da Dan Ajinsu, Hotunan Bikinsu Sun Kayatar

Ya ambaci yadda ya gabatar da ita ga abokai da yan uwansa da kuma siya mata wayar iphone 15 a makon da ya gabata.

Ya ce:

"Kin gaji. Kin gaji da me ma tukuna? Bayan na gabatar da ke ga abokai da yan uwana, kwatsam kina son mu rabu. Kina so abokaina su yi mani dariya.
"Bayan na siya maki waya a makon jiya. Kin san nawa farashin wannan wayar? Idan wasa ne ma ki daina. Na san kina son zolaya don haka hajiya idan wasa ne ki daina shi."

Martanin jama'a yayin da budurwa ta zolayi saurayi da sakon rabuwa

Mutane da dama sun taya matashin yayin da sauran suka caccaki Gracia kan zolayar saurayin nata da irin wannan lamari mai girma.

@Charmy ta ce:

"Wannan "kina son abokaina su yi mani dariya?" gaskiya ce tsantsa."

@Nkosazane_Thandekata ce:

"Gayu sun damu da abokansu sosai."

@Nthabiseng ta yi martani:

"Madam. Don Allah na zuba jari sosai a kanki."

Kara karanta wannan

'Ki Na Da Aljanu Ne?" Bayan Shekaru 2, Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ba Ya Dukanta, Bayanai Sun Fito

@Mantshangase China ta ce:

"Don Allah madam."

@Masa ya yi martani:

"Kina so abokaina su yi mun dariya ya taba ni."

@tomidew ya ce:

“Madam kawai ki daina ko ki dawo mani da wayata."

@nyambura ta ce:

"Ina bukatar saurayi dan Najeriya."

Wata mai bukata ta musamman ta haifo lafiyayyen yaro

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata mata mai bukata ta musamman ta burge mutane a TikTok bayan ta wallafa wani bidiyo na lokacin da take dauke da juna biyu.

Matar ta haihu sannan ta wallafa bidiyon dan nata don murnar gagarumin kyautar da ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel