Budurwa Ta Sharbi Kuka Bayan Saurayi Ya Fatattake Ta Daga Gidansa a Bidiyo

Budurwa Ta Sharbi Kuka Bayan Saurayi Ya Fatattake Ta Daga Gidansa a Bidiyo

  • A wani abu mai kama da rabuwa, an gano wani matashi dan Najeriya yana korar budurwarsa daga gidansa
  • Budurwar ta fashe da kuka yayin da take fafatawa da shi a kokarinta na kin son fita daga harabar gidan
  • Jama'a sun yi martani a kan bidiyon yayin da wasu mutane suka caccaki matashin kan abun da ya yi wa budurwar tasa

Bidiyon wani matashi dan Najeriya yana tura budurwarsa daga gidansa bayan sun rabu ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

A bidiyon da ya yadu a TikTok, an gano matashin sanye da farin wando da rigar shan iska, tsaye a bayan matashiyar yayin da yake tura ta daga harabar gidan.

Budurwa ta koka yayin da saurayi ya fatattake ta
Budurwa Ta Sharbi Kuka Bayan Saurayi Ya Fatattaketa Daga Gidansa a Bidiyo Hoto: @henrymoore0.0.1
Asali: TikTok

Cikin hawaye, matashiyar na ta gwagwarmaya da saurayin sannan ta ki barin harabar gidan. Wani abokin saurayin nata ne ya fito yana taimaka mata wajen fita daga gidan.

Kara karanta wannan

Hotunan Wani Katafaren Gida Da Za a Siyar Miliyan 1.5 Ya Girgiza Intanet

Da yake martani ga sukar da yake sha daga mutane, saurayin ya yi ikirarin cewa ta ci masa amana ne wanda hakan yasa shi daukar matakin a kanta. Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun fara siya mata iphone 7plus sannan muka chanja shi zuwa X, yanzu da ta ci amana mun karbi X din sannan muka mayar mata da 7plus."

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun caccaki saurayin kan abun da ya yi mata

maddieloves6ta ce:

"Don Allah ku taimakeni fa.
"Shin ni kadai ce macen da bata kuka bayan rabuwa da saurayi.
"Watakila ina bukatar addu'o'i."

Doris Kelly ta ce:

"Duk da haka ku bari mu dan ji soyayyar nan kadan koda za mu rabu kamar wannan ne akalla dai ba zai yi mana ciwo ba."

user7034756451192 ya ce:

"Ku manta da kyawun fuska mutanen nan sun iya cin amana a Afrika musamman idan ka yi masu abubuwa da dama, ni shaida ne."

Kara karanta wannan

“Rabona Da Wanka Shekara 1”: Yar Najeriya Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo, Tana Neman Agaji

Pretty benisa ta ce:

"Me zai sa ya tura ta haka mutumin da ka ce kana so."

Dan China ya gudu bayan ya yi wa budurwa yar Najeriya ciki, ta haihu

A wani labari na daban, wani dan China wanda ke zama da aiki a Najeriya ya yi wa wata budurwa yar Najeriya ciki, kuma ta haihu.

Mutumin ya kama soyayya da matashiyar a Shagamu, jihar Ogun, inda yake aiki, kuma soyayyarsu ta kai ga samun juna biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel