Matashiya Ta Wallafa Hotunan Wani Katafaren Gida a Twitter, Ta Ce Kudinsa Miliyan 1.5

Matashiya Ta Wallafa Hotunan Wani Katafaren Gida a Twitter, Ta Ce Kudinsa Miliyan 1.5

  • Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa hotunan wani katafaren gida da ta ce za a siyar naira miliyan 1.5
  • Mutane da suka ga gidan sun ki yarda da maganarta sannan cewa kudin siyan wannan katon gidan ya fi haka
  • Sun kuma ce duk mutumin da ya siya irin wannan gida yana iya fuskantar matsaloli, amma budurwar ta dage cewa ba karya take yi ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa hotunan wani katafaren gida a Twitter sannan ta ce kudin da za a siyar da shi naira miliyan 1.5.

Matashiyar, @shalomdfirst, ta haddasa cece-kuce da wannan ikirari nata, yayin da mutane da dama suka ki yarda da maganarta.

Gidan siyarwa kan miliyan 1.5
Matashiya Ta Wallafa Hotunan Wani Katafaren Gida a Twitter, Ta Ce Kudinsa Miliyan 1.5 Hoto: Twitter/@shalomdfirst and Getty Images/Tim Robberts. An yi amfani da hoton budurwar don misali ne
Asali: UGC

An kammala ginin gidan tsaf, kuma ta ce naira miliyan 1.5 ake so a siyar da shi, wanda mutane suka ce ya yi arha fiye da kima.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Saurayi Ya Yi Mata Korar Kare Daga Gidansa a Bidiyo

Mabiyanta da dama a Twitter sun zargeta da fadin karya, yayin da wasu suka yi ba'a da rubutun nata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Budurwa ta yi ikirarin naira miliyan 1.5 zai iya siyan katafaren gida

Sai dai kuma, Shalom ta dage cewa iya gaskiyarta take fada sannan ta bukaci mutane da su tayata yada rubutun don samun wadanda za su so siyan gidan.

Ta rubuta:

"Wannan gidan na siyarwa ne! naira miliyan 1.5 kacal. Don Allah ku yada."

Wasu mutane sun bayyana karara cewa duk wanda ya siya irin wannan katafaren gidan kan wannan farashin na iya fuskantar matsaloli na doka.

Kalli wallafar a kasa:

Masu amfani da Twitter sun yi martani ga katafaren gidan da aka sa a kasuwa

@MrMekzy_ ya ce:

"Da dan matsalolin kotu a nan da chan."

@mister_ade5 ya yi martani:

Kara karanta wannan

“Rabona Da Wanka Shekara 1”: Yar Najeriya Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo, Tana Neman Agaji

"Da dan matsalar mamallakan kadarar."

@oluwalonikitan ya tambaya:

"Yana da abun tsoro? Kana iya bacci da daddare a dunga daka doya a falo."

@Uniq_Rettata ce:

"Duk da haka ya yi tsada, nawa ne gaskiya?"

Budurwa ta fashe da kuka bayan saurayi ya kore ta daga gidansa

A wani labari na daban, bidiyon wani matashi dan Najeriya yana tura budurwarsa daga gidansa bayan sun rabu ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

A bidiyon da ya yadu a TikTok, an gano matashin sanye da farin wando da rigar shan iska, tsaye a bayan matashiyar yayin da yake tura ta daga harabar gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel