Hotuna: Wata biyu kacal da sakin wayar iPhone 11 a kasuwa, jaruma Rahama Sadau ta mallaketa

Hotuna: Wata biyu kacal da sakin wayar iPhone 11 a kasuwa, jaruma Rahama Sadau ta mallaketa

- Watanni biyu bayan shigowar tsadaddiyar waya Iphone 11 kasuwa, jaruma Rahama Sadau ta mallaketa

- An hango hoton fitacciyar jarumar ne a Dubai rike da dalleliyar wayar a hannunta duk da kuwa kudin wayar zai kai a kalla rabin miliyan koma ya zarce haka

- Dama can wannan al’adar ‘yan matan masana’antar Kannywood ce, shine su nuna irin wayoyin da suke rike da su a hannunsu

Watanni biyu da suka wuce ne kamfaini Apple suka saki wayar iPhone 11 a kasuwa. A cikin jaruman masana’antar Kannywood, jaruma Rahama Sadau ce jaruma ta farko mace da ta fara amfani da sabuwar dalleliyar wayar.

An ga hotunan jaruma Rahama Sadau a kasar Dubai rike da dalleliyar wayar mai kirar iPhone 11 a hannunta. Dama dai kowa yasan cewa nuna kalar wayoyin da ke hannunsu tsohuwar al'ada ce a masana'antar ta Kannywood.

Ita dai wannan wayar a kalla tana kaiwa fiye da rabin miliyan. Wayar ta shigo kasuwa ne a ranar 20 ga watan Satumbar nan da ya gabata.

Hotuna: Wata biyu kacal da sakin wayar iPhone 11 a kasuwa, jaruma Rahama Sadau ta mallaketa

Rahama Sadau
Source: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerun 'yan majalisu guda biyu a jihar Kaduna ta ce sai an sake sabon zabe

A cikin jaruman masana’antar maza kuwa, jarumi Nuhu Abdullahi ne ya fara mallakar wannan tsadaddiyar wayar.

Jarumin ya wallafa wani bidyo a shafinsa na instagram inda ya bude sabuwar wayar a kwalinta. Tuni ‘yan masana’antar da mabiyanshi a shafin sada zumuntar zamanin suka dinga tururuwar tayashi murna tare da yi mishi addu’o’in fatan alkhairi.

Hotuna: Wata biyu kacal da sakin wayar iPhone 11 a kasuwa, jaruma Rahama Sadau ta mallaketa

Rahama Sadau
Source: Facebook

Hotuna: Wata biyu kacal da sakin wayar iPhone 11 a kasuwa, jaruma Rahama Sadau ta mallaketa

Rahama Sadau
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel