Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2

Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2

  • Wata shahararriyar mai girka abinci yar Najeriya ta baje kolin abinci iri-iri a gidan abincinta sannan ta bayyana cewa farashinsu gaba daya miliyan 3.2 ne
  • Matashiyar ta fada ma mutane cewa daga cikin abubuwan da ta girka akwai shinkafa dafa duka da miyan agushi da namomi iri-iri
  • Yan Najeriya sun gaza yarda cewa za a iya kashe miliyan 3.2 a kan abinci kawai, yayin da suka fafata da ita sashin kwamet

Wata yar Najeriya mai girke-girke ta haddasa cece-kuce a tsakanin mutane bayan ta wallafa bidiyon abinciki da ya kai sama da naira miliyan 3.

Mai girkin (@hotmbycheft) ta sanar da cewar ranar zagayowar haihuwarta ne yayin da ta jefa abinciki a kan teburinta da taimakon hadimanta.

Mai girki ta baje kolin abincinta a bidiyo
Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2 Hoto: @hotmbycheft
Asali: TikTok

An baje kolin shinkafa dafa duka da soyayyiyar shinkafa

Kara karanta wannan

Hotunan Wani Katafaren Gida Da Za a Siyar Miliyan 1.5 Ya Girgiza Intanet

Daga cikin abincin da aka jera akwai robar soyayyiyar shinkafa wato 'fried rice', dafa-dukan shinkafa, miyan kaza da miyan agushi da dai sauransu a kan tebur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya da dama sun cike da mamakin cewa wannan abincin zai iya kaiwa miliyoyin nairori. Wasu kuma sun ce farashin ya yi kadan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Olatunsam ta ce:

"Akalla dai wannan ya fi siyan kifi daya a kan naira miliyan 6.8. Ya kamata Ola na Lagos ya ga wannan."

iyiolakolawolebob ya tambaya:

"Yaushe kika zama Ola na Lagos."

Chiamaka ta ce:

"Na san abinci yana da tsada amma wannan farashin ya wuce gona da iri."

Gentuuu ta ce:

"Wannan abun gaba daya 500k."

Kim namjoon ta ce:

"Bikina ya tara baki fiye da 700, Miliyan 2 da doriya aka kashe dai. Lallai da alama abokan kasuwancinki masu kudi ne."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Saurayi Ya Yi Mata Korar Kare Daga Gidansa a Bidiyo

Jane windy ta ce:

"Miliyan 3.2 nawa ake bayar da hayar kauyena gaba daya Allah ya ba da sa'a."

Budurwa ta baje kolin katafaren gidan da za a siyar miliyan 1.5

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa hotunan wani katafaren gida a Twitter sannan ta ce kudin da za a siyar da shi naira miliyan 1.5.

Matashiyar, @shalomdfirst, ta haddasa cece-kuce da wannan ikirari nata, yayin da mutane da dama suka ki yarda da maganarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel