Babbar magana: An kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu

Babbar magana: An kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu

- Wani abun al'ajabi ya afku a garin Port Harcourt inda aka kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu

- A cikin wani bidiyo da ya bazu a yanar gizo, an gano amaryar tana caccakar wanda ya kamata ya zama angon nata, inda ta bayyana cewa shine umul'aba'isin rusa farin cikinsu

- Har ila yau abokan angon sun nuna rashin jin dadinsa yayinda suka daura laifin komai a kan abokin nasu

Wani aure ya mutu tun kafin a kai ga daura shi bayan amaryar ta gano cewa mijinta na mu’amala da babbar kawarta, jaridar The Nation ta ruwaito.

A bisa ga rahoton kafafen sadarwa, rigima ta barke a birnin Port Harcourt yayinda amaryar ta yiwa angon wankin babban bargo a tsakiyar hanya tana mai zarginsa da rushe auren.

KU KARANTA KUMA: Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata

Babbar magana: An kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu
Babbar magana: An kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu Hoto: AboveWhispers
Source: UGC

A cikin bidiyon wanda ya bazu a dandalin sada zamunta, an jiyo abokan angon suna fadin cewa ‘ka kwafsa’ bayan sun tabbatar da aikata ta’asar.

Kalli bidiyon a kasa:

A wani lamari na daban, ‘Yar wasar fim, Grace Ifemeludike, ta ba mazan da su ke yaudarar matan aurensu shawarar su rungumi auren mata da yawa domin su daina lalata da mata.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa na zargin dattawan Yarbawa da kokarin haifar da tsoro da tashin hankali

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Nigerian, Grace Ifemeludike wanda jarumar Nollywood ce, ta yi wannan kira ne a shafinta na Instagram.

Da ta ke magana a ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu, 2021, Grace Ifemeludike, ta yi Allah-wadai da yadda zina ta zama ruwan dare tsakanin mazaje a Afrika.

A gefe guda kuma, wata mata mai aikin da'awah yaɗa addinin Kirista, Chinwe, ta yi watsi da ƙarar saki da aka kawo akanta a kotun gargajiya da ke zamanta a Igando Legas.

Ta kuma zargi mijinta Paul Ekwe, wanda fasto ne da aikita aikin assha da mata mambobin cocinsa kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Faston, wanda ya shigar da ƙara gaban kotun yana roƙon ta datse igiyar auren da ke tsakaninsu da matarsa Chinwe, ya zargeta da ƙulla makirci don ganin bayansa.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel