Abun Al'ajabi: Wani Bawan Allah Da Ya Roki Allah Dala Miliyan Ya Samu Kuɗi a Bidiyo

Abun Al'ajabi: Wani Bawan Allah Da Ya Roki Allah Dala Miliyan Ya Samu Kuɗi a Bidiyo

  • Bidiyon wani mutumi ya watsu a soshiyal midiya inda aka ji yana rokon Allah SWT ya ba shi dala miliyan $100m
  • Kwana biyu bayan labarin ya karaɗe ko ina, aka gayyaci mutumin wani wuri kuma ya samu taimako mai yawa daga wurin mutane
  • Duk da babu wanda ya san ainihin adadin kuɗin da ya samu amma an ga yadda jama'a suka riƙa tallafa masa a bidiyo

Wani mutumi ɗan Najeriya, wanda ya halarci taron wa'azi za aka saba yi a watan Azumin Ramadan da yamma, ya ɗaga hannu ya roki Allah SWT ya ba shi dala miliyan $100m.

Mutumin, wanda ya roƙi Allah bil hakki da gaskiya ya ba shi waɗan nan makudan kudaɗe, bai san wannan addu'a zata buɗe masa ƙofar samun taimako daga hannun bayin Allah ba.

Kara karanta wannan

An Zarge Shi da Bada Cin Hanci, Dino Melaye Ya Fadi Yadda Ya Samu Takarar Gwamna

Abun Al'ajabi.
Abun Al'ajabi: Wani Bawan Allah Da Ya Roki Allah Dala Miliyan Ya Samu Kuɗi a Bidiyo Hoto: @amirdawat
Asali: TikTok

Da alama Allah ya amsa Addu'arsa

Awanni bayan bidiyon mutumin ya watsu a kafafen sada zumunta, aka gayyace shi zuwa wani dandamalin da'awa, mutane suka dinga ba shi kyautar kuɗi masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ba'a bayyana adadin yawan kuɗin da ya tara a wurin ba amma yanayin yadda aka ga fuskarsa ta sauya zuwa fara'a lokacin da ake taimaka masa ya nuna yana da muhimmanci a rayuwarsa.

Da yawan mutanen da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa da alamun Allah ya karɓi Addu'arsa.

A cewarsu yana cikin buƙata lokacin da ya roki Allah ya kawo masa ɗauki da kuɗi kuma daga karshe ya samu.

Bidiyon ya ja hankalin mutane a dandalin sada zumuntar TikTok, kawo yanzun sama da mutane 10,000 suka kalla yayin da ɗaruruwa suka yi kwament da ra'ayoyinsu.

Kalli bidiyon lokacin da yake rokon Allah kuɗi

Kara karanta wannan

Mahaifiyar Wani Dan Najeriya Da Ke Kasar Waje Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa Bayan Cinye Kudin Da Ya Ke Aiko Mata

Bidiyon lokacin da mutane suka tallafa masa

Martanin mutane a soshiyal midiya

@Imtiyaaz ya ce:

"Kar ka taba raina ƙarfin Addu'a."

@Emjhay ya ce:

"Jinjina ga mutumin da ya ɗauki bidiyonsa ba tare da ya sani ba, Ina rokon Allah daga taskarsa mara iyaka ya lullube shi da rahama."

@ifeshola11 ya ce:

"Mutumin ya ce ko dubu 100 ne, wannan shi ake kira shugaba."

A wani labarin kuma Sarkin Musulmai ya bukaci a fara duba jinjirin watan karamar Sallah daga ranar Alhamis

A wata sanarwa da majalisar ƙolin harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ta fitar, Sultan ya ce ranar Alhamis 29 ga watan Ramadan 1444AH ne ya dace a fara duba jinjirin watan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel