“Shekara 1 Kenan Rabona Da Wanka”: Budurwa Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo

“Shekara 1 Kenan Rabona Da Wanka”: Budurwa Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo

  • An ja hankalin jama'a zuwa ga halin da wata matashiya mara galihu mai suna Mary daga jihar Ogun take ciki
  • Mary wacce ke zuba turanci kamar baturiya ta bayyana cewa bata yi wanka ba tsawon shekara guda kuma tana da matsalar rashin muhalli
  • Bidiyon ya jawo an yi kira ga masu hannu da shuni a fadin duniya da su taimaka wa Mary a lokaci da take tsananin bukatar taimako

Wata matashiya mara galihu daga jihar Ogun mai suna Mary, ta bayyana tsananin matsin rayuwa da take fuskanta duk kwanan duniya.

Da take jawabi a harshen turanci mai kyau, Mary ta bayyana kangin rayuwa da take fuskanta ciki harda cewa bata yi wanka ba tsawon shekara daya.

Mary na tsananin bukatar taimako
“Shekara 1 Rabona Da Wanka”: Budurwa Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo Hoto: @ikpabiawase/TikTok.
Asali: TikTok

Kalamanta:

"Ban san mutanen da ke yi mun magana ba, kawai dai ina jin bakin muryoyi. Ban yi wanka ba tsawon shekara daya yanzu. Ban kammala makarantar sakandare ba, na tsaya a JSS3. Ina da matsala da wajen kwana, ina bacci a karkashin furanni."

Kara karanta wannan

“Sai Kace Takobi”: Bidiyon Dogayen Takalman Wani Mutum Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mary na bukatar taimako daga al'umma

Halin da Mary ke ciki ya ja hankalin wani mai amfani da TikTok, @ikpabiawase, wanda ya yada bidiyon.

Ya yi amfani da dandamalinsa wajen kira ga masu hannu da shuni da mutane masu tausayi da su taimakawa Mary a wannan lokaci da take tsananin bukatar taimako.

Rokon gaggawa da ake yi shine a samawa Mary abubuwan bukata, muhalli, da kuma damar ci gaba da karatunta.

Kalli bidiyon a kasa:

"Ban taba sanin 'da namiji ba": Budurwa yar shekaru 36 ta sha alwashin tsare kanta

A wani labari na daban, mun ji cewa har yanzu da take shekaru 36 a duniya, matashiyar nan mai rawa da wasan barkwanci a birnin New York, Sonali Chandra, bata san 'da namiji ba.

Sai dai kuma, hakan ya janyo mata hasarar masoya da dama kamar yadda ta bayyana cewa maza basu son irin matan nan a yanzu.

Ta fada ma News.com.au cewa babban muradinta shi ne ta ci gaba da kasancewa cikin tsarki tare da kare mutuncinta na 'ya mace har sai ta isa dakin auren ta, lamarin da ke sa masu neman aurenta tserewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel