Jami’an Tsaro Sun Cafke Wani Mutum da Ya Ajiye Mata Masu Ciki 3 A Gidansa A Jihar Anambra

Jami’an Tsaro Sun Cafke Wani Mutum da Ya Ajiye Mata Masu Ciki 3 A Gidansa A Jihar Anambra

  • ‘Yan sa kai a jihar Anambra sun kama wani mutum da ake zargi da ajiye mata masu ciki har uku a gidansa
  • Ana zargin Oruchukwu Okoroafor ne da ajiye matan da kuma nufin siyar da jariran da zarar matan sun haife su
  • Yayin da ya ke martani, mutumin ya ce ba shi ne ya musu ciki ba kawai ya ajiye su ne har su haihu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Anambra – An cafke wani matashi mai suna Oruchukwu Okoroafor kan zargin girke wasu 'yan mata guda uku masu juna biyu a gidansa.

Ana zargin matashin ne da ajiye matan da kuma nufin siyar da jariran da zarar matan sun haife su.

An kama wani da zargin ajiye 'yan mata 3 masu ciki a Anambra
Dubun Wani Mutum Ta Cika Bayan An Cafke Shi Da Zargin Ajiye Mata Masu Ciki 3 A Gidansa. Hoto: The Guardian.
Asali: UGC

Ta yaya aka kama mutum a Anambra?

‘Yan sa kai ne a yankin su ka kama Okoroafor a garin Umunze da ke karamar hukumar Orumba ta Kudu a jihar Anambra inda ya ke zaune da matarsa da kuma ‘ya’yansa, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Hukuncin Zabe: Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Rufe Shaguna A Kano, Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban karamar hukumar, Neville Uchendu ya ce sun samu bayanan sirri cewa mutumin na ajiye mata masu ciki da kuma siyar da ‘ya’yan.

Uchendu ya ce ‘yan sa kai din sun shafe watanni uku su na bincike kafin tabbatar da hakaa yau, cewar Thisday.

Kama Okoroafor ya faru ne yayin da aka ganshi ya goyi daya daga cikin ‘yan matan mai shekaru 14 wacce ta kusa haihuwa a kan abin hawa zuwa wani wuri na daban.

Meye wanda ake zargin ke cewa?

Uchendu ya jagoranci mutumin zuwa wurin kwamishinar mata da jin dadin al’umma, Ify Obinabo yayin da ita kuma ta mika su ga jami’an ‘yan sanda.

‘Yan matan da ke gidan ba su wuce shekaru 14 da 19 da 20 ba wadanda su ka fito daga jihohin Bayelsa da Imo da kuma Anambra a jere.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan 'Yan Luwadi 69 Da Aka Kama Su Na Auren Jinsi, Bayanai Sun Fito

Wanda ake zargin ya bayyana cewa:

“Ba ni nake ba su ciki ba, kawai dai ni na ajiye su ne zuwa lokacin da za su haihu.
“Na gansu a wasu wurare daban inda na fahimci su na kwana a layi shi ne na dauke su zuwa gida na.
“Daman ‘yan matan su na da nufin siyar da jariransu, daya daga cikinsu har ta samu mai siya inda ya ce zai siya kan kudi Naira dubu 300 idan ta haihu.”

Ya kara da cewa ya kai shekaru biyu a gidan amma wannan shi ne karon farko da fara wannan abu.

An cafke malaman jinya kan satar mahaifa

A wani labarin, jami’an tsaro sun cafke wasu malaman jinya kan satar mahaifa a asibiti.

Wannan lamari ya faru ne a jihar Ondo inda malaman jinyan su ka hada baki da mai gadi don cimma burinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel