Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Wani Bature, Bidiyon Aurensu Ya Yadu

Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Wani Bature, Bidiyon Aurensu Ya Yadu

  • Wata budurwa ƴar Najeriya ta auri masoyinta bature, wanda ya zo daga nahiyar Turai bayan sun kwashe shekara biyu suna soyayyar nesa
  • Budurwar da masoyin na ta sun haɗu ne a yanar gizo a shekarar 2021, inda suka yi soyayyar nesa wacce ta daɗe har zuwa 2023
  • Bidiyon da ma'auratan suka sanya a TikTok ya nuna lokacin da suka yi murnar aurensu a ofishin rajistar aure na Ikoyi

Wata budurwa ƴar Najeriya ta auri masoyinta bature ɗan nahiyar Turai a ofishin rajistar aure na Ikoyi, a jihar Legas.

Masoyan masu amfani da sunan, @priscaijeomavaldgeima a TikTok, suna yin soyayya ne a yanar gizo a soyayyar nesa kafin daga bisani suka yanke shawarar su yi aure.

Budurwa yar Najeriya ta auri bature
Budurwar da baturen sun kwashe shekara biyu suna soyayya Hoto: TikTok/@priscaijeomavaldgeima
Asali: TikTok

Soyayyar nesan ta su ta kwashe tsawon shekaru biyu saboda sun haɗu da juna ne a shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Zariya, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Sun kamu da ƙaunar juna bayan sun haɗu a yanar gizo, inda yanzu suka yanke shawarar su kai soyayyarsu zuwa mataki na gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Budurwa ƴar Najeriya ta auri masoyinta bature

Wani bidiyon da aka gani a shafinsu na TikTok, ya nuna lokacin da suka yi murnar zama miji da mata.

A cikin wani bidiyon, budurwar ta bayyana cewa dogon zaman jiran da suka yi ita da masoyinta ya ƙare.

Wani bidiyon ya ƙara nuna matar auren tana nuna cikinta wanda ya yi alamar akwai jariri a ciki, wanda hakan na nufin ta samu juna biyu.

Ƴan Najeriya sun taya ma'auratan murna

Ƴan Najeriya a TikTok sun garzaya sashen bayani domin taya ma'auratan murnar abubuwan alherin da suka samu.

@gifyJo ta rubuta:

"Awwww! Allah ya sanya ku samu tagwaye da ƴan uku sannan ya cika gidanku da farin ciki da jindaɗi."

Kara karanta wannan

“Babu Miji, Babu ‘Da”: Budurwa Yar Shekaru 30 Ta Fashe Da Kuka a Bidiyo, Ta Bayyana Damuwarta

@Favour Akoma728 ta rubuta:

"Ina taya ku murna. Wai ni rigar amare wasu shafaffu da mai ne kawai ake ba? Saboda gaba ɗaya rayuwata na yi mafarkin samunta."

Ango Ya Saka Siket Zuwa Wajen Daurin Aurensa

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan Najeriya ya zo da abun mamaki bayan ya je.wajen ɗaurin aurensa sanye da siket na mata.

Angon dai ya yi shigar ne wacce ta ɗauki hankula lokacin da zai yi wuff da budurwarsa baturiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel