Wata Mata Ta Fadi Yadda Ta Samu Juna Biyu Daga Neman Mijinta Ya Mata Tausa, Bidiyon Ya Yadu

Wata Mata Ta Fadi Yadda Ta Samu Juna Biyu Daga Neman Mijinta Ya Mata Tausa, Bidiyon Ya Yadu

  • Budurwa 'yar Najeriya ta bayyana yadda ta samu juna biyu ba ta shirya daukar cikin ba nan kusa
  • Budurwar mai suna Adebola ta wallafa faifan bidiyon a TikTok inda ta ce daga neman a matsa mata jiki shikenan ta ganta da juna biyu
  • Mutane da dama sun yi martani inda su ke shawartarta da sake neman a matsa mata jiki nan gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta bayyana yadda ta samu juna biyu bayan mijinta ya taba ta.

Budurwar mai suna Adebola ta ce ta nemi mijin ya matsa mata jiki ne kawai, kafin ta ankara sai gata da juna biyu, Legit ta tattaro.

Budurwa ta fadi yadda ta samu ciki daga yin tausa
Wata Mata Ta Fadi Yadda Ta Samu Juna Biyu Daga Yin Tausa, Bidiyon Ya Yadu. Hoto: TikTok/@adebola_t.
Asali: TikTok

Ta ce ta yaya mutum zai nemi a matsa masa jiki amma a karshe ya dawo mai juna biyu wanda ko kadan ta ce ba ta shirya daukar cikin ba a yanzu.

Kara karanta wannan

Wata Mai Bukata Ta Musamman Ta Haifi Santalelen Yaro, Ta Nunawa Duniya Shi a Bidiyo

A cikin bidiyon, ta nuna kyakkyawar jaririyar da ta haifa mai suna Aila da kuma takardan gwajin cikin a wancan lokaci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ku kalli bidiyon a kasa:

Ta ce ta shiga shafin TikTok ne don bayyana yadda ta samu ciki kamar yadda kowa ke bayyana ra'ayinsu ta yadda su ka samu mazajen aure da sauransu.

Mutane sun yi martani inda su ke ba ta shawari ta sake neman a matsa mata jiki.

Martanin mutane kan bidiyon na budurwar:

@Eme Henshaw:

"Kun ci nasara."

@cassie:

"Mafi yawanci wannan matsa jikin na zuwa da karshe mai dadi."

@yuhjaybeautyville:

"Kan dan karamin tausa, kun ci wannan kalubale."

@Opeyemi:

"Ahh Mama, wannan shi ne karshen labarin? Ya yi kyau sosai."

@Zola:

"Don haka ki sake neman a miki tausa, kin gane."

@Olanshile: a

Kara karanta wannan

“’Ya’ya Maza Nake Haifa Ba Mata Ba”: Matar Aure Ta Yi Tinkaho a Bidiyo Yayin da Ta Je Ganin Filayen Mijinta

"Daga karamin tausa, ka mai da shi yaki, babu wanda zai amince ka matsa masa jiki, ki kara neman tausa jinjirar ta samu kanwa."

Jami'ar soja ta dauki juna biyu, ta nuna katon cikinta

A wani labarin, wata jami'ar soja mai dauke da juna biyu ta nuna katon cikinta a wani faifan bidiyo inda ta ke tika rawa a gaban jama'a ba kunya.

Matar mai suna Kaxandre ta kuma nuna wa jama'a yadda ta kware ta fannin iya rawa da tsalle-tsalle.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel