Wani Mutum Da Ke Zuwa Aiki a Keke Ya Fashe Da Kuka Bayan Kamfani Ya Yi Masa Kyautar Mota a Bidiyo

Wani Mutum Da Ke Zuwa Aiki a Keke Ya Fashe Da Kuka Bayan Kamfani Ya Yi Masa Kyautar Mota a Bidiyo

  • Wani bidiyon TikTok da ya yadu ya nuno halin da wani mutum ya shiga bayan ya samu kyautar tsaleliyar motar Benz daga mai kamfanin da yake aiki
  • Mutumin ya nuna jajircewarsa ta hanyar zuwa aiki duk da cewar tayar kekensa ta fashe a hanya
  • Kamfanin da yake aiki ya yi masa kyautar mota, wanda ya karba tare da nuna muhimmancin hakan a gare shi a cikin bidiyon

Wani bidiyo mai tsuma zuciya ya nuno halin da wani mutum ya shiga bayan mai kamfanin da yake aiki ta yi masa kyautar tsaleliyar mota kirar Mercedes Benz a ranar zagayowar haihuwarsa kuma bidiyon ya yadu a TikTok.

Mutumin ya nuna tsantsar biyayyarsa da jajircewa ta hanyar zuwa wajen aiki a kan lokaci, duk da cewar ya samu tayarsa ta yi faci a hanyarsa ta zuwa aiki kuma ba zai iya sauya ta da kansa ba.

Kara karanta wannan

“Ban Mutu Ba Lokacin Da Suka Binne Ni”: Lamarin Mohbad Ya Dauki Sabon Salo Inda Wani Ya Ga Mawakin a Mafarki

Mai kamfani ta gwangwaje ma'aikaci da kyautar mota
Wani Mutum Da Ke Zuwa Aiki a Keke Ya Fashe Da Kuka Bayan Kamfani Ya Yi Masa Kyautar Mota a Bidiyo Hoto: TikTok/@tiktokjamaica
Asali: TikTok

Mai kamfanin da yake aiki ta yanke shawarar yi masa alkhairi da kyautar mota, wanda aka faka a wajen ofishinsu.

Mutumin ya cika da mamaki wannan al'amari, sannan ya yi mata godiya sosai da sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma nuna godiyarsa a kan motar yana mai nuna tsantsar sha'awarta a cikin bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon mai kamfani da ta yi wa ma'aikacinta kyautar mota

NoLifekingz ya ce:

"Bayan watanni 2 ya siyar da motar marsandin sannan ya siya honda, gas, kudin inshora da na kula da motar sun fi karfin albashinsa."

Annie ta rubuta:

"G3 awww imma an tsara ne ko akasin haka, godiyar da ya nuna shine ya fi komai."

Mana ta yi martani:

"Allah ya albarkaci ma'aikatan Mac Donald da suka yi wa mutumin nan bazata."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yaron Da Hanjinsa Suka Bace Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

ChrisNYC ya yi martani:

"Allah ya yi maku albarka. Yanzu abun da yake bukata kawai shine lasisin direba."

Lorax Born:

"Nawa masu kamfanin McDonald suke samu da za su iya ba mutum sabuwar Marsandi?"

Ncebakaz93Nceba:

"Nima ina kuka. Ina ji a jikina duk shiri ne suke yi. Ba za ka ce mun bai ji lokacin da motar ke fakawa a kusa da shi ta baya ba."

Samari uku sun duka gaban budurwa don neman lambar wayarta

A wani labari na daban, wani bidiyon TikTok mai ban dariya ya yadu a intanet, inda ya nuno wani dabara mai ban mamaki da wasu matasa uku suka yi amfani da shi don samun lambar wayar wata budurwa da suka hadu da ita a hanya.

Matasan da suka yi magana a Yarbanci sun durkusa a gaban budurwar sannan suka fara yi mata addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel