An Sako Matar Da Aka Yi Wa Daurin Wata 8 Saboda Satar Riga a Adamawa

An Sako Matar Da Aka Yi Wa Daurin Wata 8 Saboda Satar Riga a Adamawa

  • Wata mata a jihar Adamawa, Zuwaira Yusuf, ta shaki iskar yanci bayan shafe tsawon watanni takwas a gidan gyara hali
  • Kotun majistare ce ta yanke mata hukuncin shekaru biyu a gidan yari bayan ta saci riga da wani kulan zuba abinci
  • An sako ta ne sakamakon sassaucin da ta samu daga kwamitin JDC na jihar mai alhakin rage cunkoso a gidan yari

Jihar Adamawa - An sako Zuwaira Yusuf daga gidan gyara hali na Hong da ke karamar hukumar Hong a jihar Adamawa bayan ta shafe watanni takwas a ciki kan sace riga da kulan abinci.

An sako matar da ta saci riga daga gidan gyara hali
An Sako Matar Da Aka Yi Wa Daurin Wata 8 Saboda Satar Riga a Adamawa Hoto: Tribune Online
Asali: UGC

An garkame Zuwaira saboda satar riga a jihar Adamawa

Kotun majistare dake karamar hukumar Gombi ta yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari kuma ta kasance a tsare tun bayan yanke mata hukuncin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Saka Dokar Kulle Na Awanni 24 a Jihar Kano

An saki Zuwaira ne lokacin da kwamitin JDC a jihar Adamawa karkashin jagorancin babbar mai shari’a, Honarabul Hafsat Abdulrahaman ya ziyarci gidan yarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun a makon jiya ne kwamitin JDC ta Adamawa ke zagayawa gidajen gyara hali a jihar a aikinta na sakin fursunoni, musamman wadanda ke jiran shari’a wadanda ake ganin shari’o’insu sun cancanci a yi musu sassauci.

Kamar yadda jaridar Daily Post ta rahoto, kwamitin ya sha bayar da belin wasu fursunoni da yake ganin sun cancanci haka, a yunkurinsa na rage cunkoso a gidajen yari, kamar yadda gwamnatin jihar ta ba da umarni.

Wani mutum ya ci na jaki kan sace mazakuta a Abuja

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutum mai suna James, ya tsallake rijiya da baya a hannun wasu fusatattun matasa a ranar Laraba kan zargin sace mazakutar wani mutum a Gwagwalada a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Bayan Yanke Hukuncin Kano, Majalisar Dokoki Ta Fara Yunƙurin Tsige Mataimakin Gwamnan APC

An tattaro cewa lamarin na Gwagwalada, ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safe a shahararren garejin nan na Wazobia da ke hanyar babban titin Abuja-Lokoja. '

Wani da abun ya faru kan idonsa, Josiah Gabriel, ya ce wanda ake zargin, wanda ya badda kammani a matsayin matafiyi, ya gaisa da wani fasinja a garejin sannan bayan wani dan lokaci sai mutumin ya koka cewa bai ga mazakutarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel