An Lakadawa Wani Duka Kan ‘Sace Mazakutar’ Wani Mutum a Abuja

An Lakadawa Wani Duka Kan ‘Sace Mazakutar’ Wani Mutum a Abuja

  • Fusatattun matasa sun lakadawa wani mutum duka a Abuja kan zargin sace mazakutar wani fasinja
  • Mutumin ya isa garejin motar Wazobia da ke Gwagwalada a matsayin matafiyi inda ya gaisa da wani fasinja
  • Jim kadan bayan sun hada hannu, sai fasinjan ya nemi mazakutarsa ya rasa lamarin da ya sa shi neman agaji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Babban birnin tarayya, Abuja - Wani mutum mai suna James, ya tsallake rijiya da baya a hannun wasu fusatattun matasa a ranar Laraba kan zargin sace mazakutar wani mutum a Gwagwalada a babban birnin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa abu makamancin wannan ya faru a makon jiya lokacin da aka kama wani direban bas a yankin Abaji kan sace mazakuta bayan ya yi musabaha da wanda abun ya ritsa da shi.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: An Kama a Wani Mutumi da Ake Zargi da Lalata da Ɗiyarsa, Ta Mutu a Yanayi Mai Mamaki

An lakadawa wani mutum duka kan sace mazakuta
An Lakadawa Wani Duka Kan ‘Sace Mazakutar’ Wani Mutum a Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda wani mutum ya sace mazakutar fasinja a Abuja

An tattaro cewa lamarin na Gwagwalada, ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safe a shahararren garejin nan na Wazobia da ke hanyar babban titin Abuja-Lokoja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani da abun ya faru kan idonsa, Josiah Gabriel, ya ce wanda ake zargin, wanda ya badda kammani a matsayin matafiyi, ya gaisa da wani fasinja a garejin sannan bayan wani dan lokaci sai mutumin ya koka cewa bai ga mazakutarsa ba.

Gabriel ya ci gaba da cewa:

"Lokacin da fasinjan ya koka, wasu mutane sun bi sahun mutumin da suka gaisa da shi sannan suka fara dukansa."

Shafin LIB ya rahoto cewa yan sanda da wani soja sun yi kokarin ceto mutumin daga hannun matasan yayin da wasu da ke wucewa suka yi saurin zuwa wajen da wayoyinsu domin daukar bidiyo.

Kara karanta wannan

Ana zaman dar-dar: Gini ya ruguje kan jama'a, mutum 2 suna can jina-jina a asibiti

Daga bisani yan sanda sun yi wa wanda ake zargin tambayoyi bayan an dauki mutumin da abun ya ritsa da shi zuwa wani asibiti.

Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan babban birnin tarayya, SP Adeh Josephine, ba a kan lamarin.

Kotu ta ba da belin matasa 'yan luwadi 69 da aka kama su na auren jinsi a Delta

A wani labari na daban, mun ji cewa babbar kotun da ke zamanta a Effurun da ke karamar hukumar Uvwie a jihar Delta ta ba da belin wadanda ake zargi da auren jinsi.

Matasan da aka kama su 69 a jihar su na bikin daura aure sun samu beli a jiya Talata kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel