Bayan Hukuncin Kotu: An Saka Dokar Kulle Na Awanni 24 a Jihar Kano

Bayan Hukuncin Kotu: An Saka Dokar Kulle Na Awanni 24 a Jihar Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar kulle na tsawon awanni 24 a fadin jihar
  • Wannan matakin na zuwa ne bayan kotun zaben gwamnan jihar ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf daga kujerarsa tare da ayyana Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben
  • Kwamishinan yan sandan jiha, Muhammad Usaini Gumel, ya bukaci al'ummar jihar da su bi wannan doka ko su gamu da fushin hukuma

Jihar Kano - Rahotanni sun kawo cewa an saka dokar kulle na awanni 24 a jihar Kano sakamakon hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kwamishinan yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, a cikin wata sanarwa da ya sawa hannu, ya ce an baza tawagar jami'an tsaro na hadin gwiwa a fadin jihar don tabbatar da bin dokar kullen.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban APC Ya Jagoranci Murnar Nasara A Kotun Zaben Kano, Bayanai Sun Fito

An saka dokar kulle a jihar Kano
Da dumi-Dumi: An Saka Dokar Kulle Na Awanni 24 a Jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Journalist KC
Asali: Facebook

Rundunar yan sanda ta sanar da saka dokar kulle a jihar Kano

Gumel ya ce wannan matakin ya biyo bayan umurnin da suka samu ne daga gwamnatin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bisa ga kundin tsarin mulki na rundunar yan sandan Najeriya tare da hukumomin tsaron cikin gida masu alaka don kiyaye doka da oda a jihar, rundunar yan sandan jihar Kano ta shirya dabaru a kan wannan al’amari tare da yin kira ga jama’ar mutanen kirki na jihar da su bayar da kwarin gwiwa da goyon bayan da ake bukata.
"Kan haka, ana kira ga mazauna jihar Kano da su lura cewa tuni aka baza tawagar tsaro na hadin gwiwa don shiga lungu da sako da kuma hanyar shiga da fita daga jihar don tabbatar da an bi dokar kullen na wanni 24 kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar ta wasika mai lamba K/SEC/H/435/T.1/153 da kwanan wata Laraba, 20 ga watan Satumbar 2023 fara daga karfe 6:00 na yammacin ranar Laraba, 20 ga watan Satumba zuwa karfe 6:00 na yammacin Alhamis, 21 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Hukuncin Zabe: Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Rufe Shaguna A Kano, Bayanai Sun Fito

"Za a kama duk wadanda suka take doka da kuma sanya su fuskantar fushin doka.
"A karshe, ina son yaba ma duk mutane masu son zaman lafiya a jihar Kano sannan ina umartansu da su ci gaba da bin doka domin tabbatar da doka da oda a jihar."

'Yan kasuwa sun rufe shagunansu a jihar Kano bayan yanke hukuncin kotu

Mun dai ji cewa hankula sun tashi a jihar bayan hukuncin kotu da ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

An gano mazauna jihar suna gudu don rufe shagunansu da wuraren kasuwancinsu saboda tsoron harin yan daba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel